✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi jana’izar Shugaban Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya

An yi jana'izarsa tare da binne shi a Jihar Kano.

Shugaban Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya, kuma tsohon mai neman takarar shugabancin kasa a  karkashin inuwar jam’iyyar SDP, Dokta Ibrahim Datti Ahmed, ya rasu.

Dokta Ibrahim Datti Ahmed ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Alhamis a Kano bayan ya sha fama da rashin lafiya, kamar yadda iyalansa suka bayyana.

Idan ba a manta ba shugaban majalisar kolin, na daya daga cikin wadanda tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya sa a cikin kwamitin da za su tattauna da Boko Haram kan tsagaita wuta a 2013, amma ya ki amsar tayin.

Dokta Ibrahim Datti Ahmed ya tsaya takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar SDP a lokacin Jamhuriyar ta uku.

An yi jana’izarsa a Masallacin Juma’a na Alfurqan da ke Kano, sannan aka binne shi a Makabartar Tarauni da ke birnin Kano.

Ya rasu ya bar ’ya’ya 10 da jikoki; daga cikin ’ya’yansa akwai Dokta Mukhtar Ibrahim Datti Ahmad, wani babban likita da ke zauna a Birtaniya.