✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka yi tsubbace-tsubbace don komawar Oba na Legas fadarsa

An gudanar da tsubbace-tsubbace na musamman a wani bangare na shirye shiryen komawar babban basaraken jihar Legas Oba Rilwanu Akiolu fadarsa.

An gudanar da tsubbace-tsubbace na musamman a wani bangare na shirye-shiryen komawar Sarkin Legas, Oba Rilwanu Akiolu fadarsa.

An gano sandar mulkin basaraken wanda wasu zauna-gari-banza suka dauke a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da suka kai wa fadar farmaki a sa’ilin tarzomar da ta biyo bayan zanga-zangar #EndSARS a Legas.

Olorogun Adodo na Legas rike da sandar mulkin Oba Rilwanu Akiolu, Babban Basaraken Jihar Legas.

Tuni dai jama’a da dama suka yi tir da aika-aikar da bata-garin suka yi a fadar basaraken da babu kamarsa a Legas.

Daruruwan matsafa da wasu gungun mutane daga masarautun gargajiyar na jihar sun taru a unguwar Isale Eko, inda suka gudanar da tsafe-tsafe da wasu al’adu domin komawar basaraken da sandar girmansa zuwa fadarsa.

Ana kyautata zaton Oba Rilwanu Akiolu zai koma fadarsa a ranar Laraba 28 ga watan Oktoba.

Wasu matsafan da suka hallara don yin tsubbace-tsubbace da al’adun gargajiya.