✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake alalan gurjiya

Yau kuma muna dauke ne da yadda ake girka alalan gurjiya

Jama’a barkanmu da warhaka. Yau kuma ga mu dauke da yadda ake girka alalan gurjiya.

Kayan hadi

– Gurjiya

– Manja

– Tattasai

– Albasa

– Gishiri

– Attarugu

– Sinadarin dandano

– Garin curry

– Ledar santana

– Ruwa

Yadda ake hadawa

– Za a nika gurjiya ta yi laushi sosai sai a tankade da abun tata a cire tsakin.

– A zuba manja a cikin tankadadden garin sai a kwaba da hannu sannan a zuba tafasasshen ruwa ba mai yawa ba, a kwaba sosai da ludayi.

– Sai a zuba markadadden tatasai, albasa, da attarugu da kuma kori da gishiri da kayan dandano.

– A zuba ruwa har sai kaurin kullun ya yi daidai yadda ake so.

– A zuba hadin a leda sai a kulla yadda ake so.

– Sai a dora a tukunya da ruwa a wuta, idan ruwa ya tafasa sai a zuba kullin hadin a ciki a bari har sai ya nuna.

– Idan alalen ya nuna sai a saukar daga wuta.

Shi ke nan sai ci!