✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda ake cinikin kuri’a a Ekiti, lamarin ya yi muni’

An ba da rahoton ba da kudi ko kayan abinci ga masu zabe a Ekiti

Wata gamayyar kafofin yada labarai na Najeriya da ke bayar da labarin zaben gwamnan Ekiti ta yi Allah-wadai da yadda ake saye ko sayar da kuri’u miraran.

Gamayyar, a karkashin jagorancin Cibiyar Inganta Dabarun Aikin Jarida (CJID), ta yi sukar ne a wata sanarwa da ta fitar ana tsaka da zaben na ranar Asabar.

“Wakilanmu sun lura da yawan da ya uzanta na sayen kuri’u – kama daga cinikin kuri’a zuwa ga bayar da kudi a cikin kango da rarraba buhunhunan/jakunkunan kayan abinci wa mutane bayan sun jefa kuri’a.

“Abin takaici, wakilan jam’iyyu ne suka yi uwa suka yi makarbiya wajen aikata wannan mummunan laifin zaben”.

Daga nan gamayyar ta tunatar da ’yan Najeriya game da darajar kuri’arsu, ta kuma yi kira ga al’ummar Ekiti da kada su sayar da kuri’unsu idan suna so su kare martabarsu a bisa turbar dimokuradiyya.

‘An samu ci gaba…’

Sai dai kuma gamayyar ta yaba da kokarin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) wajen gudanar abubuwa yadda ya kamata.

“Mun yaba da kokarin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) wajen tabbatar da cewa kayan zabe da malaman zabe sun isa [wuraren da ake bukatarsu] a kan lokaci.

“Saboda haka ne ma galibin rumfunan zabe suka kasance a bude kafin karfe 8.36 na safe”, inji gamayyar, wadda ta hada da Cibiyar CJID da Cibiyar Rahotanni da Labaran Binciken Kwakwaf ta Duniya (ICIR) da kafar yada labarai ta Premium Times, da jaridar Daily Trust da Nairametrics da Roundoffnews da kuma Orient Daily.

Haka nan kuma gamayyar ta yi Allah-wadai da yadda wakilan jam’iyyu suka nemi yin fito-na-fito da jami’an tsaron da suka hana kusantar akwatunan zabe don ganin wanda masu kada kuri’a suke dangwala wa.

Juya akalar masu zabe

“An lura da yadda wasu daga cikin [wakilan jam’iyyun] suke rubuta sunayen masu zabe da nufin biyan su daga bisani, an kuma bayar da rahoton yadda karfi-da-yaji suke ‘taimakon’ masu kada kuri’a; wannan kuwa ba komai ba ne illa wata dabara ta karkata akalar [masu zaben].

“Za mu so mu tunatar da jama’a cewa wannan babban laifi ne a karkashin Dokar Zabe kuma hukuncinsa shi ne tara da/ko dauri a gidan kaso.

“Muna kuma kira ga jam’iyyun siyasa da INEC su bincika wannan lamari”, inji gamayyar.

Wani lamari da gamayyar ta yaba da shi kuma shi ne cigaban da aka samu wajen amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a, wato BVAS.

“Sabanin abin da ya faru a Anambra bara, korafe-korafen da aka samu game da amfani da BVAS kadan ne.

“Inda aka samu matsala kuma, wakilanmu sun ce cikin dan kankanin lokaci aka warware”.

Bugu da kari, gamayyar ta yaba da yadda aka yi tanadi na musamman domin nakasassu da mata masu juna biyu da sauran masu rauni a cikin al’umma.

Fifiko ga masu rauni

A cewarta, an yi aiki sosai da Sashe na 54 na Dokar Zabe, domin kuwa, “wakilanmu sun ga yadda aka bayar da fifiko a layi ga mata masu juna-biyu da tsofaffi da kuma nakasassu a fiye da kashi 60 cikin 100 na rumfunan zabe.

“Sai dai kuma mun lura cewa an samu rashin amincewa da hakan inda wasu suka yi korafin cewa ba a kyauta wa sauran jama’ar da ke kan layi ba”.

A madain gamayyar dai cibiyar CJID ta tura wakilai ko masu sa-ido 28 zuwa dukkan kananan hukumomi 16 na Jihar ta Ekiti don su aiko da bayanan abin da yake faruwa.

A halin yanzu kuma wadannan wakilai suna aiko da bayanan abubuwan da suke wakana da zarar sun faru.

Don bibiyar yadda zaben na Ekiti yake tafiya kai-tsaye ziyarci shafukanmu na sada zumunta, wato facebook.com/aminiyatrust da twitter.com/aminiyatrust da kuma Instagram.com/aminiyatrust.