✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girka soyayyiyar shinkafa

Yau a filinmu na Girke-girken Azumi, za mu kawo muku yadda ake girka soyayyiyar shinkafa

Uwargida Barka da rana. Ya azumi. Yau a filinmu na Girke-girken Azumi, za mu kawo muku yadda ake girka soyayyiyar shinkafa.

Ga wasu daga cikin kayan hadin da ake bukata:

Shinkafa

Mai

Attarugu

Sinadarin dandano

Karas

Koren wake

Kori

Albasa

Yadda ake yi:

Da farko za ki samu shinkafarki ki zuba ta a mazubi mai kyau, ki zuba mata ruwa ki wanke sai ki tace ta a abin tace taliya har ta tsane, sai ki zuba mai a tukunya.a

Idan man ya dau zafi, sai ki debo shinkafarki ki zuba akan mai ki yi ta juya ta har sai kinga tayi kalar ruwan zuma, sannan sai ki kwashe  ki zuba a matsami don man ya tsane,

Amman za ki zuba attaruhu ki soya idan ya soyu sai ki zuba ruwa kadan idan ya tafasa saiki kawo shinkafarki ki zuba tare da karas da sianadarin xanxano  da kori da albasa da duk kayan qanshinki da kika tanada. Sai ki rufe ki ba ta lokaci ta xan turara. KIna yi kina dubawa har ta dahu.
Acai dadi Lfya