✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ake hada ‘juice’ na Beetroots

Beetroot na rage alamar tsufa, gyara fata, wanke ciki da jini, kara lafiyar hanta, rage hawan jini da kuma kara tsawon gashi.

Juice din Beetroot yana da amfani ga dan a matsayin kayan marmari.

Beetroot na rage alamar tsufa, gyara fata, wanke ciki da jini, kara lafiyar hanta, rage hawan jini da kuma kara tsawon gashi. Yana kuma kara kuzari, kare zuciya, rage hadarin kamuwa da cutar kansa da kuma matsalar kwakwalwa.

Ga yadda ake yin sa:

Kayan hadi

  • Beetroot
  • Citta
  • Lemo
  • Na’ana’a
  • Lemon tsami

Yadda ake hadin

1. A wanke beetroot, chita, na’ana’a, Lemo da lemo tsami da gishiri.
2. Sai a dauraye su sosai sannan a yayyanka su kanana.
3. A markada beetroot, Citta, na’ana’a da lemon tare.
4. A tace markaden a zubar da tsakin.
5. A matse ruwar lemon tsami sai a sa a ciki.
6. A ajiye hadin a firinji  ya yi sanyi
6. Beetroot ‘juice’ ya fi kyau idan aka zuba a kofin gilashi tare da kankara, sai sha.