✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ake taron bajekolin fina-finai a Saudiyya

Jarumai daga Amurka da Faransa da sauran sassan duniya sun halarci taron da haska fina-finai 138 daga kasashe 67

Kasar Saudiyya na gudanar da wani babban taron bajekolin fina-finai a karon farko inda aka shirya hasak fina-finai 138 daga kasashe 67.

Taurarin fim maza da mata daga kasashen duniya sun halarci taron a irin shigar da suka zaba wa kansu, domin daukar hoto da tattaunawa da ’yan jarida — sabanin tsarin Saudiyya na sanya bakaken abaya ga mata.

“Wannan rana ce mai dimbin tarihi a kasar Saudiyya,” inji Darktan taron, Mohammed Al Turki, a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na AFP.

An fara gudanar da taron ne ranar Litinin washegarin ranar da aka gudanar da gasar tseren mota ta duniya (Formula 1) a birin Jidda da nufin nuna kasar a matsayin mai tafiya daidai da zamani.

Taron fim din zai gabatar da fina-finai a cikin harsuna 30, kuma ya karbi bakuncin taurarin fim daga kasashen Larabawa da sauran sassan duniya, kasa da shekara hudu bayan kasar ta sake bude gidajen sinima da wuraren casu.

Daga cikin bakin da za su halarta har da daraktar fim mace ta farko a Saudiyya, Haifaa al-Mansour, wadda ta samu lashe kyaututtuka da dama daga kasashen duniya saboda da fim dinta mai suna ‘Wajda’ da aka haska a shekarar 2012.

A shekarun baya, Masarautar Saudiyya ta rufe gidajen sinima, amma ta janye takunkumin a shekarar 2018.

“Wannan wani sabon babi ne, amma muna bukatar samun kari,” inji jaruma Elham Ali a yayin da tafe sanye da wata doguwar riga a wurin taron.

“Shekara biyar da suka wuce babu wanda zai taba tunanin za a gudanar da taron bajekolin fim a Saudiyya,” inji wani mai sharhi kan adabi dan kasar Masar, Mohamed Abdel Rahman.

Tun shekarar 2017, Yarima Mai Jiran Gado na Masarautar Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya yi sauye-sauye a kasar.

Sauye-sauyen da Mohammed bin Salman ya kawo sun hada da ba wa mata izinin tuki da kuma cakuduwar mata da maza a tarukan casu.