✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ake yin ‘doughnut’

Assalamualaikum! A yau nazo muku da yadda ake hada doughnut cikin sauki. Doughnut abun ci ne ake yi da fulawa da sauran kayan hadi domin…

Assalamualaikum! A yau nazo muku da yadda ake hada doughnut cikin sauki.

Doughnut abun ci ne ake yi da fulawa da sauran kayan hadi domin marmari, tarbar baki, ko sana’a.

 • Kayan hadi:
 1. Fulawa kofi 2
 2. Gishiri cokali 2
 3. Sukari kofi 1
 4. Kwai 2
 5. Bota cokali 2
 6. Yis cokali 2
 7. Ruwa rabin kofi

 

 • Yadda ake hadawa
 1. Da farko za a sa ruwan dumi cikin kofi daya da rabi sannan a zuba yis da sukari a ciki.
 2. A rufe ruwan a ajiye shi na tsawon mintoci 15.
 3. A zuba fulawa, sukari da gishiri a kwano, sannan a fasa kwai a ciki.
 4. Daga nan sai a kawo hadin yis din a zuba a kai.
 5. Sai a sa bota a buga shi sosai saboda doughnut na bukatar bugawa sosai.
 6. Bayan haka sai a rufe a ajiye shi a wuri mai dumi.
 7. Idan ya tashi sai a sake bugawa a fitar da fasalin da aka bukata a bar shi na tsawon mintoci 15.
 8. Daga nan kuma sai a fara soyawa.

Yadda ake doughnut ke nan a cikin sauki.