✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ake yin miyar wake

Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatar ana cikin ƙoshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake miyar wake. An fi sanin Nufawa da…

Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatar ana cikin ƙoshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake miyar wake.

An fi sanin Nufawa da wannan miyar saboda ita ce miyarsu ta gargajiya. Suna kiran ta da ‘Ezowa’ watau miyar wake.

Yana da kyau uwargida ta koyi girke-girke na ƙabilu daban-daban domin hana maigida cin abinci a waje, da kuma sanya kunnensa motsi.

An fi haɗa wannan miya da tuwon shinkafa.

Abubuwan da za a buƙata
•        Wake
•        Man ja
•        Attarugu
•        Busasshen kifi
•        Albasa
•        Gishiri da magi

Haɗi
Uwargida ta samu wake ta jiƙa shi, ta cire dusarsa, ta ɗora ruwa a wuta.

Bayan ya tafasa, sai ta zuba waken ya yi ta tafasa har sai ya nuna ya yi luƙwi.

Sannan ta zuba yankakkiyar albasa da dakakken attarugu da manja da busasshen kifi bayan an wanke shi (kifin).

Sai a jira miyar ta yi ta tafasa na mintuna kaɗan, sannan a zuba magi da gishiri.

Ana iya cin wannan miyar da tuwon shinkafa.

Zai fi kyau a girka ta da rana ko da yamma.

Da fatar za a girka wa maigida wannan miyar domin armashi da ɗanɗano mai gamsarwa.