✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Anthony Joshua ya yi gaisuwar ban-girma ga Buhari

Zakaran Damben Boksin na Duniya dan asalin Najeriya da ke zauna a Birtaniya Anthony Joshua  ya zube a kasa (dubale) don yin gaisuwar ban-girma irin…

Zakaran Damben Boksin na Duniya dan asalin Najeriya da ke zauna a Birtaniya Anthony Joshua  ya zube a kasa (dubale) don yin gaisuwar ban-girma irin ta kabilar Yarbawa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a birnin Landan.

Joshua ya fada wa jama’a cewa zai tsaya tsayin-daka wajen kare Najeriya a duk lokacin da aka bukaci haka.

Mutane da dama sun bayyana mabambantan ra’ayoyi game da hotunansa yana gaisuwar da aka watsa a jaridu da kafafen sadarwar zamani, inda masu sukar Shugaba Buhari ke nuna takaici kan yadda dan damben ya ki bayyana irin dimbin kalubalen da matasan Najeriya ke fuskanta.

Sai dai tuni Joshua ya mayar da martani ta shafinsa na Instagram inda ya ce “Wannan ba batu ne na siyasa ba. Batu ne na al’ada da kuma girmama na gaba da mu.”

Wadansu kuma yaba wa Joshua suka yi kan yadda ya rungumi tsatsonsa Najeriya da kuma yadda ya nuna girmamawa ga Shugaba Buhari ta hanyar yin gaisuwar da aka san kabilar Yarbawa da yi.

Shugaba Buhari na birnin Landan ne domin halartar taron zuba jari na Birtaniya da Afirka na farko da aka fara ranar 20 ga Janairu.

Daya daga cikin masu taimaka wa Shugaba Buhari, Tolu Ogunlesi, ya wallafa wasu hotunan taron a shafinsa na Twitter inda ya ce: “AJ! Shi da Shugaban Kasa a yau.”