✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda auren dana zai kasance da matar sa Ba’amurikiya’

Malam Suleiman ya ce auren tsakanin dan nasa da matar tasa mai shekaru 46 zai gudana a masallaci.

Mahaifin matashin nan dan asalin Jihar Kano da ke dab da angwancewa da amaryarsa ’yar asalin kasar Amurka, Malam Suleiman Isah ya ce bikin dan nasa zai gudana ne bisa tanade-tanaden addinin Musulunci.

Ranar Lahadi mai zuwa, 13 ga watan Disamban 2020 ne za a daura auren a unguwar Panshekara da ke Kano.

Aminiya ta gano cewa annobar COVID-19 ce dai tun da farko ta kawo wa bikin tsaiko, wanda da aka tsara yin shi a watan Maris din da ya gabata.

Malam Suleiman ya ce za a daura auren dan nasa, Isah Suleiman da amaryar tasa, Misis Janine Sanchezt mai shekara 46 ne a cikin masallaci.

“A cikin masallaci za a daura auren, kuma mu za mu biya ta sadaki kamar yadda Musulunci ya yi tanadi”, inji Malam Suleiman.

Sai dai mahaifin matashin ya ce saboda kalubalen tsaro da ake fama da shi a kasa, bikin zai gudana ne ba tare da wasu shagulgula na ku-zo-ku-gani ba.

“Na ma hana su yin kowane irin shagalin fati a bikin. Ina tunanin mata ’yan uwansa ne kawai za su yi yinin biki domin taya dan uwansu murna”, inji shi.

Kazalika, mahaifin angon mai jiran gado ya ce sakamakon matsalar rashin samun bizar tafiya Amurka ga dan nasa, amaryar ita kadai za ta koma da zarar an daura auren daga bisani shi kuma ya biyo bayanta.

Idan dai za a iya tunawa, Janine da Isah sun fara haduwa ne a dandalin sa da zumunta na Instagram kimanin shekara biyu da suka wuce suka kuma fara soyayya ka’in-da-na’in.

Ko a watan Janairun da ya gabata sai da Ba’amurikiyar ta yi takakkiya har birnin Kano domin ta hadu da iyayen masoyin nata kafin a kai ga amincewa a kulla aure a tsakaninsu.

Tuni dai Misis Janine, wacce take zaune a birnin California na Amurka ta sauka a Kano tun ranar Juma’a a shirye-shiryen bikin nasu ranar Lahadi mai zuwa.

A baya dai, matar ta shaida wa Aminiya cewa tsabar soyayyar da take wa Isah ce ta sa ta yanke shawarar aurensa.

Shi dai Isah, wanda yanzu haka yake shekararsa ta farko a jami’a ya ce a shirye yake ya bi matar tasa zuwa Amurka domin ya fara sabuwar rayuwa tare da gina sabon iyali a can.