✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Buhari zai sa hannu kan kasafin 2021

Ranar Alhamis zai sa hannun kan kasafin 2021 na Naira tiriliyan 13.58

A ranar Alhamis 31 ga watan Dismaba, 2020 Shugaba Buhari zai rattaba hannu a kan kasafin kudin Najeriay na 2021 da Majalisar Tarayya ta amince da shi a makon jiya.

Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya shaida wa wakilin Aminiya hakan, bayan a ranar Litinin ce Fadar Shugaban Kasa ta tabbatar da cewa Majalisar Tarayya ta mika mata kudurin dokar kasafin na 2021.

A zaman gaggawar da Majalisar Tarayya ta yi kan kasafin ranar Litinin din makon jiya ne ta amince da kasafin kudin 2021 na Naira tiriliyan 13.58, bayan zaurukanta na Dattawa da Wakilai sun amince da rahohon Kwamitocinsu na Kasafin.

Masu sharhi na hasashen sanya hannu kan kasafin zai ba da damar komawa ga aiwatar da kasafin kudin Najeriya daga watan Janairu zuwa Disamba a duk shekara.

Ana sa ran Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokokin Majalisar Dattawa, Babajide Omoworare da takwaransa kan Majalisar Wakilai, Umar El- Yakub ne za su gabatar wa Shugaba Buhari kundin kasafin kudin domin ya rattaba hannu a kai.

Garba Shehu ya ce Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila da sauran shugabannin Majaliar Tarayya za su halarci sanya hannun.

Shugabannin Kwamitocin Kasafi na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai tare da ’yan Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) na daga cikin mahalarta zaman na ranar karshe a shekarar 2020.

Mahalarta zaman daga FEC su ne Minisatar Kudi, Kasafi da Tsare-tsaren Kasa, Zainab Ahmed; Minista a Ma’aikatar, Clement Agba; Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele; Darakta-Janar na Ofisihin Kasafi na Kasa, Ben Okabueze da sauransu.

Sai dai babu tabbacin ko mahalartan za su hallara ne a zahiri ko ta bidiyo, duba da yanayin COVID-19.