✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda fasinjoji suka ceto yara 5 da ‘wata ‘yar sanda’ ta sato daga Sakkwato

An bukaci hukumomin Jihar Sakkwato su bi diddigin lamarin don ceto yaran.

’Yan sanda a yankin Birnin Tarayya Abuja sun fara gudanar da bincike a kan wasu mata biyu da ake zargi da satar yara kanana 5 daga Sakkwato zuwa Abuja.

Yaran da suka hada da wata jaririya ’yar mako biyu da haihuwa da wasu yara hudu da dukkansu ba su wuce shekara 2 ba, sai daya mai shekara uku.

Ana zargin an sato yaran ne a ranar Asabar da ta gabata daga wata unguwa mai suna Kwannawa, a birnin Sakkwato, kamar yadda daya daga cikin fasinjojin motar da aka dauko yaran, Abba Danbaba ya shaida wa Aminiya, kuma ya ce, daya daga cikin wadanda ake zargi da sato yaran ’yar sanda ce da ke aiki a Abuja, amma ta tafi har Sakkwato ta taho da yaran.

Tuni aka kama matan biyu masu suna ASP Kulu Dogonyaro da take aiki a Sashen Kula da Yara da Mata na Babban Ofishin ’Yan sandan Kubwa, Abuja da abokiyar zarginta Elizabeth Ojo, inda ake ci gaba da gudanar da bincike.

‘Yadda muka gano akwai matsala’

Da yake yi wa Aminiya karin haske a kan yadda lamarin ya auku, Abba Danbaba ya ce, motar da suka shigo ta taso ne daga Tashar Alu da ke Unguwar Dandima zuwa Abuja tare da matan biyu da ake zargi da kuma yaran.

Ya ce, “Da farko Elizabeth din ce ta zo ta biya kudin kujera uku, inda ta shaida wa masu lodi cewa, ragowar fasinjojin za a dauke su ne a kan hanya.

“Ana isa Kwannawa sai ta biyun wato Kulu ta taho da jaririya goye a bayanta tare da rakiyar wata mata da kuma yara hudu.

“Sai ta shigo motar, muka wuce tare da matan biyu da yaran, ita kuma dayar ta koma.”

“To yanayin kukan jaririyar a motar da rashin ba ta mama da ’yar sanda da ke rike da ita ta gaza yi ne, ya sa muka fara tunanin akwai matsala.

“Mun ga ta ki ba ta mama, sai dai ta rika ba ta madarar roba, kuma ga jaririyar karama ’yar makonni.

“Wannan ne ya sa wasu mata biyu da ke kusa da su a cikin motar, suka fara zargin akwai lauje a cikin nadi,” in ji shi.

Ya ce, “To bayan mun tsaya a garin Funtuwa, inda aka ci abincin rana, a nan ne maganar ta kai ga sauran fasinjoji da kuma direba cewa ana zargin wadannan matan biyu da sato kananan yaran.”

Abba ya ce, ‘‘Bayan sun iso Abuja mata biyun sun nuna za su sauka a garin Deidei, amma sai direban motar ya ki tsayawa a wajen har sai da matan suka fara korafi tukuna tare da ta da hankalinsu a kai, sai ya tsaya a gari na gaba mai suna Kagini.’’

Ya ce, bayan an tsaya ne sai ya fuskanci mata biyun tare da shaida musu cewa ba a gamsu da dangantakarsu da yaran ba, saboda haka dole a gudanar da bincike a kai.

Abba ya ce, ya wuce zuwa karamin ofishin ’yan sanda da ke garin Kagini kafin a mika lamarin ga babban ofishin ’yan sanda da ke garin Gwagwa, inda aka ci gaba da tsare su har zuwa ranar Litinin kafin a wuce da su zuwa hedikwatar ’yan sanda da ke Abuja.

Ya ce, tuni matan suka amsa cewa yaran ba ’ya’yansu ba ne, wani ne mai suna Bala a garin Sakkwato ya hada su.

Ba wannan farau ba Aminiya ta samu labarin cewa, ’yan sanda na shirin kai samame zuwa gidan daya daga cikin matan a Unguwar Deide da ke Abuja, inda ake zargin akwai wasu yaran a gidan.

Wani bayanin daban da Aminiya ta samu ya nuna cewa, gabanin wannan lamari ma an gano cewa, daya daga cikin matan ta taba zuwa waccan tashar motar ta Sakkwato, inda ta shiga mota, sannan ta bukaci a tsaya a hanya domin ta dauki wasu yara kamar yadda ta yi a wannan karo.

Babbar Jami’ar Hulda da Jama’a ta Rundunar ’Yan sandan Abuja, S.P Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike a kai.

Wani jagoran kungiyar fafutikar kare hakkin al’umma, mai suna Kwamared Nura Mukhtar da ya fara tsegunta wa Aminiya labarin ya ce, za su ci gaba da sa-ido tare da bin kadin al’amarin har sai sun tabbatar da adalci.

An mayar da binciken zuwa Sakkwato

A yayin da ’yan sanda a Abuja ke shirin kai samame zuwa gidan daya daga cikin wadanda ake zargin, sai aka samu labari a ranar Talatar da ta gabata cewa, an mayar da aikin binciken zuwa hedikwatarsu a Jihar Sakkwato.

Babban mai shigar da korafin, wanda daya ne daga cikin fasinjojin motar sufurin da aka dauko yaran a ciki, wato Abba Danbaba ne ya shaida wa Aminiya haka.

Ya ce, hakan na zuwa ne bayan shigar da wata kara a kan lamarin da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta yi kan bukatar gudanar da binciken daga can.

Ya ce, wani ayarin ’yan sanda daga Sakkwato ya isa Hedikwatar Rundunar ’Yan sandan Abuja a ranar Talata bayan ya taho a ranar a jirgin sama kan bukatar a mika masu wadanda ake zargin da kuma yaran, inda ya ce tuni aka amince da bukatar.

Ya ce, an ji ’yar sandan tana cewa ba ta fargabar mayar da lamarin zuwa Sakkwato tare da yin alwashin cewa za ta kubuta a can.

Ya ce, a yanzu babban abin damuwar shi ne watsi da shirin kai samame zuwa gidan daya daga cikin wadanda ake zargin da ke Deidei, sakamakon mayar da binciken zuwa Sakkwato, duk da ana zargin akwai wasu yaran a can Deidei din.

Sai ya bukaci hukumomin Jihar Sakkwato su bi diddigin lamarin don ceto yaran tare da tabbatar da an hukunta wadanda ake zargin.