✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Jihar Legas ta samar da kamfanin sarrafa shinkafa mafi girma a Afirka

Yanzu kamfanin shi ne irinsa mafi girma a Afirka, na uku a duniya

A ranar Litinin, Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani katafaren kamfanin sarrafa shinkafa, irinsa mafi girma a nahiyar Afirka mallakin jihar Legas.  

Kamfanin , mai suna Lagos State Imota Rice Mill, da ke Imota a unguwar Ikorodu wanda yake mallakin Jihar ne, shi ne irinsa  mafi girma a Afirka kuma na uku mafi girma a duniya.

Tun a shekarar 2017 Gwamnan Jihar na wancan lokacin, Akinwunmi Ambode, ya bayyana shi a matsayin kamfanin sarrafa shinkafa mafi girma a Najeriya yayin kaddamar da fara shirin aikinsa.

Kamfanin zai rika sarrafa shinkafa mai nauyin metric tan 32 a kowane awa, tare da  samar da buhun shinkafa miliyan 2.5 a duk shekara tare da samar da aikin yi ga mutanen Jihar sama da 250,000.

Kamfanin ya shirya samun danyar shinkafa da ba a gyara ba daga jihohin Kwara da Sakkwato da Binuwai da Borno da Kebbi, inda zai rika sarrafa ta kuma yana sayarwa a ko’ina a fadin Najeriya.

Abin da ya sa gwamnatin Legas ta samar da kamfanin

Jihar Legas ta yi duba da cewa shinkafa na daya daga cikin manyan kayan abinci da ke samar da riba mai yawa ga manoma da kuma yadda ake cin shinkafa a kasar, ya sa ta yi kokarin samar da irin wannan kamfani domin kara habaka tattalin arzikin jihar da kuma kasa baki daya.

A wata kididdiga ta Thrive Agric, ta gano cewa galibi manoman shinkafa na sayar da kaso 80 cikin 100 na abin da suke nomawa inda suke cin abin da bai wuce kaso 20 ba kawai.

Hakan ya sa shinkafa ta zama abincin da ke samar da kudin shiga ga manoman Najeriya fiye da duk wani amfanin gona a kasar.

Ana sa ran kamfanin zai bunkasa samar da shinkafar da aka tace ‘yar gida da za ta yi gogayya da sauran manyan kamfanonin shinkafa na duniya a kasuwa.

Tun farkon kafa Gwamnatin Shugaba Buhari a 2025, ta mayar da hankali ne wajen bunkasa harkar noma da kuma samar da abincin da ‘yan kasa za su ci a cikin gida Najeriya.