✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda jinin al’ada ke hana ni zuwa makaranta —Daliba

Halin da daliban sakandare mata ke shiga a yayin jinin al’ada, albarkacin zagayowar Ranar Yara Mata ta Duniya karo na 10

Wata dalibar sakandare ta ce a duk lokacin da take jinin al’ada tana zama ne wuri daya, ko makaranta ba ta iya zuwa a tsawon kwanakin.

Joyce Daniel mai shekara 18, daga Makarantar Sakandaren Ladi Atiku a Jihar Adamawa, ta shaida wa Aminiya cewa, ba ta iya zuwa ko’ina idan tana jinin al’ada saboda tsoron kada ta bata kayanta da jini ko kuma wani ya ga jini a jikinta.

Ta ce yayar mahaifiyarta ce ta fara sanar da ita game da jinin al’ada da yadda za ta kula da jikinta idan ya zo mata da yadda ake sanyawa da kuma canza augudar al’ada.

Hakika ganin fitowar jini daga al’aurar yarinya abin tashin hankali ne, musamman a wurin wadda ba ta da labarin jinin al’ada da yadda za ta kula da kanta a irin wannan yanayi.

’Yan mata da yawa — da ma wasu manyan mata — musamman a karkara na fama da matsalar karanci ko ma rashin audugar al’ada da sauran abubuwan da suke bukata domin tsaftacewa da kuma kula da kansu idan suna haila.

A sakamakon haka, da dama daga cikinsu kan kasance cikin takura a tsawon lokacin da suke haila, saboda gudun kada jinin ya bata su, ko a gani a bainar jama’a.

Hakan ne kan da wasunsu yin kunzugu domin tare jinin da abubuwan da ke iya cutar da rayuwarsu.

A kan haka ne Joyce, a hirarsu da Aminiya, ta yi kira ga gwamnati da ta taimaka da samar da ruwa domin mata su rika samun sakewa a duk lokacin da suke al’ada.

Aminiya ta zanta da dabibar da takwarorinta ne domin jin halin da suke shiga idan suna haila, da yadda suka fara ganin jinin da kuma abin da suka yi a lokacin.

Mun tattauna da su ne albarkacin zagayowar Ranar Yara Mata ta Duniya karo na 10, wadda ake yi a duk 11 ga watan Oktoba, don wayar da kai game bukatun ’ya’ya mata da bayar da hakkokinsu da samar musu abubuwan da suke bukata da kuma ba su kwarin gwiwa a kan abin da suke yi da wadanda suke neman su cimma a nan gaba.

Yadda jini ya fara barke min

Jinin haila kan iya barke wa mace a kowane lokaci kuma ko’ina, musamman ga wadda ba ta taba yi ba kuma ba ta san alamominsa ba.

Joyce ta shaida wa wakiliyarmu cewa haila ta fara zuwa mata ne a lokacin da take tsaka da wanke-wanke a gida.

Ta ce da ta  fara ganin jinin sai ta sanar da mahaifiyarta, wadda ita kuma ta yi mata bayani a kan yadda ake kula da kai.

Ita ko Aisha Abubakar Balla ta ce a lokacin da ta fara ganin jinin haila, tana cikin aiki ne, ta ji cikinta yana ciwo, can da ta duba sai ta ga jini a jikinta.

Da ta sanar da mahaifiyarta dangane da abin da ya gani, sai mahaifiyar ta bayyana mata cewa  jinin al’ada ne sannan ta koya mata yadda ake yi ida ya zo.

Game da yadda nata jinin al’ada ya fara zuwa, Hauwa Mustapha, ta ce, “Na fara jin ciwon ciki, sai washegari na ga jini a gabana.”

Abin da na yi bayan ganin jini

Hauwa ta ci gaba da cewa, “Sannan na sanar da mahaifiyata inda ta tabbatar min da cewa girma ya taddo ni, da kuma yadda zan rika kulawa da kare kaina.

“A ranar da na fara ganin jinin haila na fada wa mahaifiyata, sannan ta sanya ni a kan hanya, kan ta yadda zan tsaftace jikina, ta ba ni su turaren shafawa da dai sauransu.”

Ta ci gaba da cewa, “Mahaifiyar tawa ta sake tunatar da ni game da yadda ake wankan daukewar jinin haila da yadda zan rika kintsa jikina da kuma kin yin hulda da maza.

“Ta tsoratar da ni, inda ta ce kada na bari namiji ya kama [ko da] hannuna, in ba haka ba zai iya zama min matsala, hakan ya sanya nake taka-tsantsa.”

A Islamiyya na fara sani

Sabanin Joyce Daniel wadda innarta ce ta fara yi mata bayani kan jinin al’ada, its Hauwa mai shekara 17, ta ce a makarantar Islamiyya ta fara samun labarin jinin kafin balaga ta zo mata.

“Da yake muna zuwa Islamiyya ana dan fada mana, amma ba a bayyana mana sosai ba.

“Kamar yadda aka sanar da ni, cewa aka yi idan mace ta fara ganin jini a jikinta, ta hanzarta wajen fada wa mahaifiyarta.”

Dalibar ta ce haila ba ta hana ta zuwa makaranta, saboda a makarantarsu akwai ruwa a makewayi da za su yi amfani da shi domin tsaftace jikinsu idan suna jinin al’ada, “musamman idan mace ta san yadda za ta kintsa jikinta.”

Ita ma Fatima Zahra Sani mai shekara 16, ta ce a makarantar Islamiyya ta fara sanin labarin jinin haila da yadda za ta kula da kanta da kuma yadda ake wankan tsarki.

Game da yadda nata ya fara zuwa ta ce wata rana bayan ta farka daga barci sai ta ga jini a jikinta, daga nan ta fada wa mahaifiyarta, sai ta ba ta audugar al’ada ta sanya.

Yadda ake kula da dalibai masu haila a makaranta

Malam Adamu Buba Muhammed wanda ke koyarwa a Makarantar Sakandare ta Ladi Atiku, ya ce “Akwai wata yarinya ’yar SS1 wadda ciwon ciki ya dame ta har ta gagara zama a aji.

“Sai muka kai ta ofishin firinsifal, daga nan aka kira wata malama wadda ta gane cewa yarinyar jinin haila ne ya zo mata.

“Ko da aka tambayi dalibar ko ta taba yi sai ta ce wannan ne karon farko da take ganin jini a gabanta.

“Daga nan sai ita shugabarmu a makarantar ta ce na ba su wuri domin matsalarsu ce ta mata.”

Malam Adamu ya ce, “Da ma akwai audugar al’ada da ake amfani da ita wadda wata kungiya ta ba da, sai aka ba dalibar ta saka kafin aka kai ta gida.”

Haila na hana dalibanmu zuwa makaranta

Malamin ya ce akwai dalibansu da haila ke hana su zuwa makaranta.

Ya ce ita kanta dalibar da yake maganar an taimaka wa, sai da ta yi kwana uku sannan ta ci gaba da zuwa makaranta.

Ya kara da cewa ko sun tambayi daliban nasu dalilan rashin zuwansu makaranta cewa suke ciwon ciki ne ke hana su.

A cewar malamin, makarantar tana tanadar audugar al’ada na zamani kasancewar wasu daliban jinin ka zo musu ne ba tare da sun sani ba, kuma akwai kungiyoyi da suke kawowa kyauta.

Sai dai ya ce rashin isasshiyar audugar al’ada na hana wasu dalibansu zuwa makaranta.

“Mukan sayi ruwa a amalanke kafin mu samu borehole domin akwai randar da muke ajiye musu ruwa wani sa’in ma kusa da randunansu muka ajiye [musu audugar] saboda suna jin kunya.

“Amma yanzu muna da ruwa ba mu da matsala,” in ji malamin makarantar.

‘Kafin su balaga ya kamata a sanar da su’

Wata mahaifiya, Yagana Ali, ta ce, “Duk yarinya da ta fara tasowa kafin ta balaga, ya kamata uwa ta zaunar da ita ta sanar da ita abubuwan da ke kunshe a rayuwa.”

A cewarta, tun yarinya tana ’yar shekara 10 ya kamata iyaye suna dan zantawa da ita daga lokaci zuwa lokaci.

Ta ce, “Wasu na fara jinin haila da wuri, wasu kuma yana dan jinkiri;  Yawanci mafi karancin shekaru da yara suke farawa kamar shekara tara ne zuwa 10, wadda kuma ya dan jinkirta yana kaiwa 14.

“A wannan lokacin ya kamata uwa ta sanar da yarinya yadda za ta kula da kanta idan wannan abun ya faru.”

Yagana ta ce a lokacin da suke yara, akwai wata da abin ya taba fito mata kuma ba ta da masaniya a kansa, har yara suka taru.

Ta ce, “Idan an shirya yaro da cewa makamancin haka na iya tasowa sannan idan ya faru ga yadda zai yi yana da kyau.

“Amma yanzu iyayenmu sai su ga kamar ka zauna ka yi magana irin wannan da yaro rashin kunya ne, ko kuma rashin sani ne.

“Ko kuma an jahilce tarbiyar yaran ne?

“Wasu iyayen ma ba su sani ba, wata (yarinyar) har ta fara ta yi wankin zani biyu, uku ma uwar ba ta san ta fara ba, watakila idan [’yar] ta dan bata kayanta ne za ta gani.”

Ta gargadi iyaye da su farga su sanar da ’ya’yansu yadda ya kamata su tsaftace kansu.

“Tun da sun riga sun sani, idan balagar ta zo komai ya wajaba a kan yaro kamar yadda ya wajaba a kan babba a Musulunci — su azumi da Sallah duk sun hau kansu.”

Har yara maza…

Ta ce ba mata ba kadai, har da yara maza ya kamata iyayensu maza suna janyo su a jika suna fada musu ababen da ya kamata domin kada su hadu da abokan banza da za su iya lalata su.

Bukatar su san hukunce- hukunce

Amirar Kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) Reshen Jihar Adamawa, Khadija Buba, ta ce daga lokacin da yarinya ta fara jinin haila, to duk dokokin addinin Musulunci sun hau kanta.

“Da zarar ta balaga, to duk abin da babba ke yi na Kur’ani da Hadisi ita ma ya hau kanta — ta aikata ababen da aka ce a yi da kuma kin aikata ababen da addini ya hana.”

Ta yi kira ga yara mata wadanda suka fara haila da su tabbata sun iya wankan tsarki da kuma tsaftace jikinsu.

“Kamar yadda aka koyar da mu tun muna yara muna zuwa karatun allo, idan mun tashi akwai Islamiyya ana karantar da mu saboda haka wadannan abubuwa tun kafin ka girma ka san dokoki da kuma yadda za ka kintsa jikinka,” in ji ta.

Ta ce duk yarinyar da ta  fara haila kuma ba ta da labarinsa, idan ta ga jini a gabanta sai ta sanar da mahaifiyarta domin su iyaye za su nuna mata yadda za ta kintsa jikinta.

Amira ta ce idan suna da kudin sayen audugar al’ada ta zamani sai su saya su kuma koyar da ita da kuma sanin yadda za a canza shi saboda kada ya janyo ciwon sanyi.

Ta ba da shawarar yin wanka sau uku a rana idan akwai ruwa, idan babu kuma a yi wanka sau biyu da kuma sanin lokacin canza audugar saboda idan ya dade yana janyo kuraje da cututtuka wani sa’in ma harda hana haihuwa.