✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda karyayyar gada ta ci rayuka 21 a Jigawa

Akalla mutum 21 ne aka tabbatar sun mutu bayan da motocin da suke ciki suka fada cikin wata karyayyar gada a kauyen Rabadi da ke…

Akalla mutum 21 ne aka tabbatar sun mutu bayan da motocin da suke ciki suka fada cikin wata karyayyar gada a kauyen Rabadi da ke Karamar Hukumar Gwaram ta Jihar Jigawa.

Lamarin dai ya faru ne dai misalin karfe 1:00 na daren ranar Asabar, inda ya ritsa da motoci biyu dauke da fasinjoji 22 a kan hanyar Gwaram zuwa Basirka.

Da take tabbatar da lamarin ranar Lahadi, rundunar ’yan sandan Jihar ta ce ya faru ne lokacin da wata motar Bas mai lamba FYK 406 ZA Gombe da za ta tafi Jihar Adamawa dauke da fasinjoji 18 daga Jihar Kano da kuma wata motar kirar Kanta mai dauke da mutum uku suka fada karyayyar gadar.

Baturen ‘Yan Sandan yankin (DPO), SP Yusuf Wakili ya ce wadanda iftila’in ya shafa na kan hayarsu ne daga Kano bayan halartar neman tantance masu son shiga aikin sojan kasa, amma basu yi nasara ba.

Ya kara da cewa takardun da suka samu daga matafiyan sun nuna mafi yawa daga cikinsu daga Jihar Adamawa suke, sai kuma mutum dai-daya daga Jihohin Taraba da Borno.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Aliyu S. Tafida, tare da rakiyar Mataimakin Kwamishina mai kula da ayyuka da sauran jami’an rundunar suma sun ziyarci wurin inda suka ba da umarnin gudanar da bincike nan take kan lamarin.

Shi ma Mataimakin Gwamnan Jihar, Umar Namadi wanda shi ma ya jagoranci sauran jami’an gwamnatin Jihar inda suka ziyarci wajen ya umarci a fara kokarin lalubo iyalan mamatan domin a mika musu gawarwakin ’yan uwan nasu.