✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mahara suka kashe ’yan sanda 4 da wasu 44

’Yan bindiga sun kashe mutum akalla 48 sun tashi kauyuka takwas a karshen mako.

Akalla mutum 48 ne ’yan bindiga suka kashe, ciki har da fararen hula 44 da jami’an ’yan sanda hudu a jihohin Zamfara da Ebonyi a karshen mako.

’Yan bindiga a Jihar Zamfara sun harbe ’yan sanda biyu a ofishin ’yan sanda na Magami da ke Karamar Hukumar Gusau, sai Jihar Ebonyi inda aka binidige ’yan sanda biyu a Babban Ofishin ’Yan Sanda na Ugbuodo a Karamar Hukumar Ebonyi.

Hare-haren ’yan bindiga sun kuma lakume rayukan fararen hula 44 daga ranar Juma’a zuwa safiyar Lahadi a jihohi takwas, baya ga mutum 14 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna.

’Yan bindiga sun hallaka akalla fararen hula 21 a Jihar Zamfara, 12 a Jihar Neja sai Jihar Filato inda suka kashe mutum biyar a wadannan kwanakin.

Sun kuma kashe mutum uku aJihar Sakkawato, mutum biyu a Adamawa sai Jihar Delta da Ebonyi inda aka kashe mutum daya-daya.

Baya ga haka an kashe wasu mutum uku da ake zargi da satar mutane a Jihar Adamawa bayan ’yan banga sun rutsa su a wata kasuwa.

Rahotanni sun ce wadanda ake zargin sun yi wa ’yan bangar turjiya ne, lamarin da ya sa mutane suka yi musu taron dangi suka kashe su.

Sakkwato: An kashe mutum 3 an tashi kauyuka 8

A Jihar Sakkwato ’yan bindiga sun kashe mutum 3 a kauyen Garin Zogo a Karamar Hukumar Sabon Birni, inda suka tashi kauyuka takwas.

Kansilan yankin, Ibrahim Muhammad Saraki ya ce an kai wa Garin Zogo harin ne da misalin 10:30 na daren Asabar.

“Sun kashe mutum uku sun jikkata daya, sun sace dabbobi sun kuma fasa shaguna sun sace kayan da ba a san iya adadinsu ba,” inji shi.

Ya ce washegari, ranar Asabar, maharan sun kai farmaki a kauyukan Nasarawa da Gidan Idi da Rambadawa inda suka jikkata mutum uku suka kuma sace shanu.

A cewarsa, ’yan bindiga sun rika bi gida-gida suna yi wa mutane fashi, har kayan jeren daki ba su bari ba.

Kansilan ya ce, “Saboda kashe-kashen da ake yi mana a kullum sun sa yanzu ba ma kwana a gidajenmu, sai dai mu je kauyen Sabon Birni mu kwana washegari mu dawo, ciki har dani.

“Yanzu haka duk mutane sun yi kaura daga kauyukan Rambadawa da Garin Idi da Tudun Wada da Nasarawa da Tamindawa da Garin Ango da Tsaunar Dogo da Tashalawa.”

Ya roki gwamnati ta kawo musu dauki saboda yadda ’yan bindigar suka addabi yankunan.

Mataimakinsa na musamman, Lamiru Umar, ya ce wasu mazauna yankunan sun yi hijira zuwa kauyen Tsululu da ke Jamhuriyar Nijar.

An nemi kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Sunusi Abubakar kan lamarin amma an kasa samun sa a waya.

Wakilanmu: Sagir Kano Saleh da Faruk Shuaibu da Kabiru R. Anwar da Amina Abdullahi, Yola da Abubakar Auwal, Sakkwato da Ado A. Musa, Jos da Shehu Umar, Gusau  da Muhammad I. Yaba, Kaduna.