✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Na kashe mutum 3, na caka wa 25 makami —Dan shekara 16 mai kwacen waya

Duk da cewa ’yan sanda sun kama ’yan daban 1,220 sun kwace daruruwan makamai, masu kwacen waya sun kashe rayuka, mutanen da suka raunata sun…

Wani saurayi mai sheka 16 da aka kama yana kwacen waya bayan kwana 20 da rasuwar mahaifinsa, ya ce ya kashe mutum uku, ya kuma caka wa wasu 25 makami.

Saurayin, wanda ya ce tun yana makarantar karamar sakandare ya shiga harkar dabanci da shaye-shaye ya ce, idan ya ritsa mutanen da yake wa kwacen waya, tun kafin ya ce su kawo wasunsu suke miko nasu.

Aminiya ta kuma zanta da wani mai shekara 28 da ya shekaransa takwas yana kwacen waya; Duk da cewa an taba kai shi gidan yari, yanzu haka an sake kama shi.

Mun kuma gana da mutanen da suka fadawa a hannun masu kwacen waya ko masu kwacen waya suka kashe musu makusanta a Kano kan irin halin suka shiga.

Kwacen waya a Kano

Akowane lokaci, cikin dare ko rana al’ummar birnin Kano suna cikin fargaba musamman wadanda ya zame dole su hau keken Adaidaita Sahu (Keke NAPEP), ko masu tafiya a kafa domin tsoron yin arba da masu kwacen waya.

Wadanda suka fi yin wannan aika-aika ta kwacen waya matasa ne da ba su wuce shekara 20, da a lokuta da dama suke dauke da makamai da suka hada da wukake da sauransu.

Daga Unguwar Bachirawa zuwa Na’ibawa; Kabuga zuwa Kofar Mata; Titin Gidan Zoo zuwa Titin Hadeja; Sabon Gari zuwa Gwale; Kofar Kudu zuwa Titin Gidan Gwamna da ma yawancin unguwannin da suke cikin birnin Kano suna fama da wannan matsala ta masu kwacen waya wadanda za a iya cewa suna cin karensu babu babbaka.

Lamarin ya yi kamari inda a kwanakin har da rana ma akan yi kwacen wayar.

Sun fito da sababbin hanyoyin kwacen wayar

A yanzu kuma sun bullo da wasu sababbin hanyoyi na kai wa mutane hari inda suke rufe hanyoyi ko gadar sama ko ta kasa su yi kwacen.

Yawancin matasan suna shayeshaye, sannan suna barin mutanen da suka farwa da raunuka har da rasa rai.

A watannin baya akalla mutum biyar aka hallaka bayan kwace musu waya.

Kano wadda ita ce cibiyar kasuwanci ta Arewa kuma masaukin wadansu ’yan kasuwa da ke shigowa daga makwabtan kasashe da suka hada da Nijar da Chadi tana fama da matsalar yawan al’umma.

Bayan mutanen da suke tuttudowa a kullum, akalla akwai mutum miliyan 40 da suke cikin birnin Kano, idan aka hada da masu shigowa a kullum babu yadda za a iya hana aikata laifuffuka iri-iri.

Sharifatu bakuwa ce daga Jamhuriyar Nijar da aka taba yi wa kwacen waya a bainar jama’a a Kano.

Duk da cewa jihar na yi wa kanta kirari da jihar da ta fi samun kwanciyar hankali a Arewa maso Yamma, yankin da ke fama da matsalar ’yan bindiga, al’ummar jihar suna da abin yaka.

A kididdigar da Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta bayar, ta ce ta kama ’yan daba akalla 1,220 a wata 11 da suka gabata.

Duk da cewa ba dukkan ’yan dabar suke kwacen waya ba, amma mafi yawansu an kama su ne saboda kwacen waya da laifuffukan da suke kama da haka.

Majiyar ’yan sanda ta shaida wa Aminiya cewa yawancin wadanda ake kamawa ’yan siyasa da shugabannin al’umma ne suke wuc musu gaba wajen neman belinsu.

Abin da ya sa muke kwacen wayar — Wadanda aka kama

Aminiya ta tattauna da wadansu daga cikin wadanda aka kama kan zargin kwacen wayar.

Muhammad Auwal mai kimani shekara 28, dan Unguwar Dala ne, ya ce idan ya yi shayeshaye zai ji shi a “a sama” wanda hakan ke kai shi ga yin kwacen waya da sauransu.

Ahmad ya ce ya shiga wannan harka ce tsawon shekara 10 da suka gabata inda har aka taba kama shi da laifi a kotu aka yanke masa hukuncin dauri a gidan gyaran hali. Sai dai maimakon Ahmad ya gyaru sai ya sake koyo wasu sabbin hanyoyin kwace wayoyin.

Duk da cewa bai taba kashe mutum ba kamar yadda ya bayyana, ya ce ya sha yi wa mutane rauni ta hanyar yin amfani da wuka.

Wannan matashin ya shekara kusan 10 yana kwacen waya duk da cewa an taba kai shi gidan yari a kan laifin.

Ya ce, “A duk lokacin da na kwaci waya nakan je in sayar da ita a Kasuwar ’Yan Waya. Kuma wadansu daga cikin masu sayen suna sane cewa wayoyin na sata ne. Mafi yawa daga cikinsu ba su sani ba.

“Idan aka sayar da wayoyin kudin ba wani yawa gare su ba, idan aka kwatanta da ainihin kudinsu, amma haka nan nake karba saboda ina bukatar kudi don in sayi wiwi da kodin da wanda zan ba ’yan matana.”

Ya ce iyayensa ba su san yana satar waya ba sai dai sun san yana shaye-shaye kuma suna yi masa addu’a a kan ya daina. “Yanzu haka sun san ina hannun ’yan sanda amma sun ki zuwa saboda ina ba su kunya,” inji shi.

Ya ce, akwai wani lokaci da ’yar uwarsa ta kira ’yan sanda don su kama shi lokacin da wayarta ta bata kuma a cewarsa shi ne ya dauki wayar domin har ya kusa sayarwa.

Ya ce a mafi yawan lokuta yana hawa kan Dutsen Dala ne inda yake haduwa da abokansa suna aikata laifuffuka ta hanyar yi wa mutane fashin kayayyakinsu a gidaje da kuma kan titi.

Da yake bayanin yadda ya fara shaye-shayen miyagun kwayoyi, Ahmad ya ce ya fara ne a Abuja lokacin da yake zaune a gidan kawunsa.

“Ni da kake ganina ina da ilimin boko da na addini. Lokacin da babana ya gaji da halina sai ya tura ni Abuja wurin kawuna wanda ya sama min makaranta ina zuwa ina kuma taimaka masa a harkar kasuwancinsa.

“To daga nan ne na fara shaye-shaye. Lokacin da na dawo Kano kuma sai na hadu da abokaina da muke zuwa kan Dutsen Dala,” inji shi.

Ya ce: “Wannan ne karo na uku da aka kama ni. A wancan lokacin muna yara ba mu tunanin komai amma a yanzu na yi hankali idan Allah Ya yarda wannan shi ne na karshe. Yanzu na fahimci cewa ni ne matsalar gidanmu kuma na riga na bata musu suna.”

Na kashe mutum uku

Shi kuma Usman Sa’idu mazaunin Unguwar Jakara mai kimanin shekara 16 ya ce yana da hannu a kisan akalla mutum uku a kwacen waya.

Sa’idu wanda ya daina zuwa makaranta tun a karamar sakandare ya ce tun daga lokacin da ya fara wannan harka shekara uku da suka wuce ya kai wa akalla mutum 25 hari tare da kwace wayoyinsu.

Ya ce shi da abokansa suna gudanar da wannan ta’asa ce a kan hanyar Mandawari zuwa Jakara.

“Yawancin lokuta mun fi yin abinmu da yawa domin mu tsorata mutane don su ba mu wayar cikin sauki.

“Mu ba kudi muke karba ba, sai waya domin mun san ba kowa ne ke tafiya da kudi ba, amma kowa yana tafiya da wayarsa. Yawancin matasa su ne wadanda muka fi kai wa hari saboda su ne suke amfani da manyan wayoyi,” inji shi.

Matashin da ya kashe mutum uku, aka kama shi yna kwacen waya bayan kwana 20 da rasuwar mahaifinsa.

Sa’idu wanda ya ce an taba kama shi amma mahaifinsa ya yi belinsa, ya ce an yi masa wannan kamu ne mako uku bayan rasuwar mahaifinsa.

Ya ce, mahifinsa bai san irin laifuffukan da yake aikatawa ba saboda a lokacin da ya yi belinsa ya yi ne a kan fada da suka yi da wani abokinsa. Bai san cewa dansa yana kashe mutane ba.

Sa’idu ya ce, “Na fara shayeshaye ne dalilin wani abokina inda muke haura katanga a Makarantar Sakandaren Gwale musamamn idan an fito Sallah sai mu je mu yi shaye-shayenmu sannan mu koma makaranta.

“Daga baya ma sai na daina zuwa makarantar gaba daya na rika bin wannan abokin nawa zuwa wasu wuraren da mukan hadu da wadansu abokan. Nakan gan su da wukake sai suka fada min inda zan samu in saya.

“A Sharada na fara sayen wuka. Har ila yau wadannan abokan namu su suka sa ni a hanyar satar waya.”

A cewar Sa’idu wasu lokuta yakan yanki mutane da wuka ba tare da ya kwaci waya ba. “Wani lokacin ina shiga cikin abokaina in yanki mutane da wuka don kawai mu yi dariya,” inji shi.

Yadda suke kutse a wayoyin da suke sace

Baya ga rashin waya da mutum yake yi da fargabar da yakan shiga sakamakon kwace masa wayar, a yanzu kuma masu satar wayar sun hada kai da masu kutse a Intanet don su kara wa mutumin zafi.

Bincike ya nuna cewa masu kwacen wayar a yanzu suna sayar da layin wayar, inda su kuma za su samu damar kutsawa cikin asusun ajiyar bankin mutumin su sace masa kudinsa.

Bincike ya nuna cewa masu kutsen suna iya shiga asusun ajiyar mutum ta hanyar yin amfani da lambar sirrinsa ta BBN da ta manhajar USSD wacce ke ba su dama su shiga asusun ajiyar bankin mutum tare da kwashe masa kudi tan hanyar sayen katin waya da sauransu.

Bincike ya nuna cewa wadansu da ke kwacen wayar ‘masu kirki’ sukan sayar wa mutum layin wayarsa kafin su yi awon gaba da wayar.

Dalilin da lamarin ke kazanta —Malamai

Talauci da rashin aikin yi da hadama da rashin wadatar zuci da rashin yin hukunci mai tsauri su ne abubuwan da suke sa wadannan laifuffuka suke karuwa, kamar yadda malamai da shugabannin al’umma suka bayyana.

Sheikh Mujitaba Abubakar Ramadan shi ne Limamin Masallachin Juma’a na Gidan Gwamnatin Jihar Kano, ya bayyana cewa, “Duk wanda yake da tarbiyya da kyawawan halaye ba zai shiga harkar shaye-shaye ba ballantana ya fara kwacen waya.”

Shi kuwa Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya bayyana cewa rashin kulawa da matasa daga gwamnati shi ya janyo suka shiga wannan lamura.

Har ila yau duk da cewa ana kama irin wadannan kayan maye daga dilolin kwayoyin da kuma masu amfani da su har yanzu harkar shaye-shayen sai karuwa take yi.

Sheikh Tijjani Bala Kalarawi, ya danganta yawaitar matsalar a kan shaye-shaye da rashin kulawar gwamnati.

‘Halin da muka shiga bayan kwace mana waya’

Tun lokacin da Hauwa Salisu Ahmad mai shekara 30 da kanwarta Hidaya Salisu Ahmad mai shekara 25 suka hadu da bala’in kwace rayuwarsu ta shiga wani yanayi da ba su taba zato ba.

Al’amarin, wanda ya yi sanadiyyar rasa ran dan uwansu, ya bar Hauwa cikin tsananin fama da ciwo wanda har ila yau, ba ta iya tsayawa da kyau ko yin Sallah a tsaye.

Al’amarin ya faru ne da dare ranar 27 ga Ramadan din shekarar 2020 a hanyarsu ta zuwa masallaci Sallar Dare.

“Ko nisa ba mu yi ba, sai wadansu ’yan Adaidaita Sahu suka zo wucewa. A tunaninmu su ma masallacin za su je, sai wani daga cikinsu ya ce masallaci za ku? Ba mu ba su amsa ba, kafin mu ankara sai suka sauko suka zagaye mu.

“Saukowarsu ke da wuya suka umarce mu da mu kawo wayoyinmu. Muna nuna turjiya suka zaro makamai. A rayuwata ban taba ganin makamai irin wadannan ba. A take na razana na fadi na suma. Suka sassari dan uwanmu namijin da yake tare da mu.

“Da suka fahimci mun fara ihu za mu tara musu mutane sai suka koma cikin Adaidaita Sahun su suka gudu,” inji ta.

Cikin rashin sani ga Hauwa da ’yan uwanta, ashe wadanda suka zo kawo musu dauki su ma tare suke da wadancan da suka tafi wadanda su ma ganin mutane sun fara tunkaro wurin suka gudu.

“Namijin da yake tare da mu yanzu haka ya rasu. Tun wancan lokaci ni ma ban sake tsayawa da kafafuwana na yi Sallah ba,” inji ta cikin sanyin murya.

’Yar uwarta, Hidaya Salisu Ahmad ta ce, “A lokacin da Hauwa ta fadi ta suma, maharan sun yi tunanin karya take yi ko wani salon dabara ce, hakan ya sa suka soke ta da wuka suka kuma kwace wayoyin da ke hannunta.”

Washegari bayan sun je wajen ’yan sanda ne suka fahimci cewa suna cikin mutum 9 da aka yi wa makamanciyar wannan ta’asa a wannan dare.

Hauwa, ta shafe watanni a asibiti kafin ta samu kanta.

Ta kara da cewa, “Har yau, idan na ga bakuwar fuska, ba na natsuwa ko yarda da mutum musamman idan na ga yana tunkaro ni, sai jikina ya fara rawa. Haka duk lokacin da na ga wani ya fito da wayarsa a kan hanya sai wannan al’amari ya dawo min a zuciya.

“Mun shaku matuka da dan uwana da ya rasu sanadiyyar haka, mutum ne mai saukin kai da kirki.

“Ba na iya tsayuwa in dade ko in dauki abu mai nauyi. Ba na iya sunkuyawa saboda ciwon da nake da shi da ya shafi kashin bayana. Lokuta da dama idan ciwon ya tashi da wata na’ura nake amfani domin samun sassauci,” inji ta.

Ta kara da cewa wannan hari ya taba aikinta na koyarwa. Sakamakon haka sai dauke ta daga aji aka yi ta koma ma’aikatar ilimi domin ci gaba da gudanar da aiki a ofis.

Hauwa ta ce tana addu’ar shiriya ga matasan idan masu shiryuwa ne.

“Mahukunta kuma, ina addu’a Ubangiji Ya ba su dama da kwarin gwiwar yaki tare da shawo kan wannan annoba,” inji ta.

Mutane da dama a cikin gari da kewayen Kano suna da labarai iri-iri da suke da alaka da kwacen waya da za su bayar kamar Hauwa da Hidaya.

’Yan uwan wadanda aka kashe sanadiyar kwacen waya na ciki jimami

’Yan uwa da abokan arzikin wani matashi tela mai shekara 30, Abdullahi Bala har yanzu suna cike da alhinin yadda matashin ya rasa ransa sakamakon haduwarsa da masu kwacen waya.

Haka ’yan uwan marigayi Umar Muhammad, ma’aikaci a Hukumar Adana Kayan Tarihi, wanda shi ma ya rasa ransa sakamakon kwacen waya a watan Yulin bara har yanzu suna alhinin rashinsa.

‘Yadda muka tsira da ranmu daga masu kwacen waya’

Matasa irin su Abba Ibrahim Wada da Abdullahi Aliyu Hamza da Saddika Rabi’u da Abdussamad Is’hak da Zainab Nasir Ahmad da A’isha Abubakar da Zubairu Abubakar ba za su taba mantawa da artabun da suka yi da matasan masu ban tsoro da rashin imani ba. Al’amarin da suka ce zai dauki lokaci mai tsawo kafin su manta da shi.

‘Yadda tsoho da matashi suka kwace min waya’

Sau uku Abba Ibrahim Wada (Abba Gwale) a cikin shekara biyu yana arangama da wadannan miyagu a wurare daban-daban. Na karshen shi ne wanda ya fi daga masa hankali saboda wanda ya kai masa harin tsoho ne mai shekara kusan 60.

“Al’amarin ya faru ne lokacin ina cikin Keke NAPEP na taso daga wajen aiki daga Titin Murtala Muhammad zuwa Gwammaja. Lokacin da na hau akwai fasinja daya a ciki. Bayan mun fara tafiya wani tsoho mai kimanin shekara 60 ya tare mu ya hau.

“Bayan mun hau doguwar gadar sama ta Sabon Gari sai tsohon nan ya shake ni yana cewa in kawo wayata. A lokacin ne na fahimci daya fasinjan da matukin babur din duk tafiyarsu daya da wannan tsoho.

“Daya fasinjan sai ya ciro wuka ga shi kuma tsohon nan ya shake min wuya. A kokarin kwatar kaina na yi nasarar tura tsohon nan waje ni ma na yi tsalle na fice daf da sauka gada,” inji shi.

Abba Ibrahim Wada ya yi arba da wani tsoho a cikin masu kwacen waya, amma ya sha da kyar a hannunsu.

Abba ya ce duk lokacin da ya ji labarin kwacen waya da ya hada da jin rauni ko kisa yakan shiga dimuwa sosai ganin shi ma a lokuta daban-daban da kyar ya sha.

Shi ma Abdussamad yayin arangama da masu kwacen wayar, ya ce sun taba kwace masa sabuwar waya mai tsada a ranar da ya sayo ta ko gida bai karasa ba.

Ya ce a yayin da wayarsa ta salwanta, mai babur din da ya dauko shi an ji masa rauni tare da tafiya da Adaidaita Sahunsa.

Sai dai ya ce su biyun ba su kai kara ga ’yan sanda ba domin suna ganin bata lokaci ne. Ya ce sau uku yana haduwa da masu kwacen waya amma sau daya suka samu nasara.

A’isha Abubakar daliba ce a Jami’ar Bayero da ke Kano, ta ce, rasa wayarta ga masu kwacen waya da ta yi ya yi matukar taba karatunta.

Kwanaki kalilan bayan rasa wayar, an yi yunkurin nemo ta inda aka gano har an kai ta Jihar Binuwai. Sai dai ta ce ta gode wa Allah da ta tsira da lafiyarta.

Abin da muke yi don shawo kan matsalar —’Yan sanda da gwamnati

A tattaunawa da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano, Sama’ila S. Dikko ya ce tun lokacin da ya kama aiki, matsalar kwacen waya a jihar ya yi kasa, kuma rundunar ’yan sandan jihar tana kokarinta wajen magance matsalar baki daya. Ya ce gano wurare masu hadari da kama masu aikata laifin shi ne abin da sashen Operation Puff Adder ya sa a gaba.

“Haka kuma akwai shiryeshiryen wayar da kan jama’a a gidajen rediyo da talabijin da ake yi, kuma hakan na samar da nasarar da ake da bukata,” inji shi.

Kwamishinan ya ce rundunar ta yi nasarar dakile harkokin shan kwaya da sauran kayan maye wanda shi ke assasa wadannan laifuffuka har ta kai ga kama masu sayar da kwaya mutum 120 a cikin wata 11.

Ya ce, “Abin dadin shi ne muna kokarin samo asalin inda masu aikata wadannan laifuffuka suke tare da dakatar da abin daga nan. Mun yi nasarar kama manyan dillalan kayan maye kuma mun mika su ga Hukumar NDLEA.”

A cikin masu kwacen waya akwai mutane wadanda suka kware wajen iya kutse a cikin bayanan sirri na mutane da wadannan wayoyi da suke karba a hannunsu. Kuma rundunar ta yi nasarar kama manyan masu kutse har 25.

Mai magana da yawun Gwamnatin Jihar Kano, Abba Anwar ya bayyana a wata hira da ya yi cewa gwamnati tana kokarin yaki da matsalar baki daya.

Ya ce gwamnati ta kafa na’urorin sa-ido a wurare da dama da ake kula da su daga Hedikwatar Rundunar ’Yan sandan Jihar.

Anwar ya ce, “Ire-iren wadannan laifuffuka sun shahara a birane da dama da ke fadin duniya. Wannan ya sa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen dakile su.

“Hakan ya sa gwamnati ta shirya wani taron kara wa juna sani ga jami’an tsaro domin ganin an yaki rashin aikin yi da shayeshaye.

“Domin haka ne ma gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a zangonta na farko ta tallafa wa matasa miliyan daya tare da wasu shirye-shirye domin dogaro da kai.

“Sannan gwamnati ta gina wuraren koyon sana’o’i 24 domin tallafa wa matasa,” inji shi.

Ya ce a kokarinta na kawar da shaye-shaye, gwamnatin ta kafa kwamitin yaki da fataucin kayan maye a kasuwanni kuma masu sayar da magaunguna za su koma inda za su gudanar da kasuwancin su cikin tsafta.

Yadda za a shawo kan matsalar

Lura da yadda lamarin yake jefa fargaba a zukatan mutane, masana da malamai da al’ummar gari sun ba da shawarwari don shawo kan matsalar kwacen waya da sauran matsalolin ta’addanci da suke addabar al’umma.

Mukhtar Nura Bichi, masani ne a kan tsaro a Jami’ar Bayero da ke Kano. Ya ce yadda al’ummar jihar ke fama da rashin aikin yi da yadda matasa suke yawon banza a tituna, dole ne a sa ido a kan wadannan matasa tare da taimaka wa ’yan sanda.

Shi kuwa shehin malami, Tijjani Bala Kalarawi cewa ya yi, “Idan har muna so mu kawar da munanan dabi’u a cikinmu, to dole doka ta yi tasiri a kan masu aikata laifuffuka ba tare da duban wane ne ko dan wane ne ya aikata ba.”

Ya kara da cewa, “Wadannan yara, dole a sama musu katangar da za su jingina da ita su daina yawon banza a titi.”

A bayanin, Malam Mujitaba Ibrahim Abubakar Ramadan ya ce canjatunani ga al’umma yana da matukar tasiri wajen yaki da wannan mummunar dabi’a.

“Kwacen waya annoba ce wadda a kullum take haddasa rasa rayukan mutane. Hukuma dole ta tashi tsaye domin abu ne da za a tambaye su ranar tambaya.

“Hakkinsu ne su kula da kare hakkin mutane da kayansu a matsayinsu na shugabanni. Abu ne da kullum yake haddasa fargaba ga dubban al’umma.

Daga Clement Oloyede da Salim Umar da Lubabatu Garba