✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda maza suke sakar wa mata daukar nauyin gida

Wani magidanci yana kwance a gida, zai aiki matarsa kanti ta sayo masa abin da yake bukata

Babu shakka ɗaukar nauyin gida kacokan ya rataya ne a kan miji, ya alla a addinance ko a al’adance.

Wannan lamari haka yake a kusan dukkanin addinai da al’adu, sai dai ɗan bambancin da ba za a rasa ba.

Ana ganin ita kanta kalmar miji ta samo asali ne daga kalmar majibincin lamari, mai nuni da yadda miji yake ɗaukar nauyin iyalinsa dari bisa dari tun daga kan abinci da suttura da kula da lafiya da ilimin ’ya’ya da sauransu.

Hakan ya sa idan aka zo daurin aure ake bayyana wa ango ko wakilinsa cewa ciyarwa, shayarwa da tufatarwa sun tashi daga kan iyaye sun koma kansa.

Sai dai za a iya cewa a yanzu wannan lamari yana neman ya kau sakamakon yadda maza da dama suke sakin ragamar kula da gida a hannun matansu, lamarin da ake ganin ba zai haifar da kyakkyawan ba a cikin al’umma.

Irin wannan yanayi ya jefa rayuwar matan a cikin damuwa da shiga halin ni-’ya-su lura da nauyin da ake ɗora musu wanda yake fin ƙarfinsu.

Za a iya kasa sha’anin miƙa ragamar kula da gida ga mata zuwa kashi biyu:

Akwai yanayin da matan da kansu su suka nemi a bar musu harkar gidan ta yadda suke kallon hakan a matsayin wani abu na ’yanci.

A irin wannan yanayi mazan kan ba mata kuɗin gudanar da harkokin gida tun daga kan kayan abincin gidan da sauransu.

A irin wannan za a samu mace ce ke zuwa kasuwa don sayen duk wani abin amfanin gida, hatta suturar da iyalan gidan ke sanyawa matar ce ke sayowa.

Haka ɗawainiyar kaiwa da komowa na karatun ’ya’ya za ka tarar matar ce ke gudanarwa.

A wannan yanayi ko auren ’ya’yanta za a yi, matar nan da ake damƙa wa lamarin auren kacokan a hannunta musamman harkar sayen kayan ɗaki da abincin gida da sauransu.

A kashi na biyu kuma za a samu mazan ne da kansu suke sakar wa matan harkar kula da gidan ba tare da suna bai wa matan wani abin a-zo-a-gani na ɗawainiyar gidan ba.

A irin wannan yanayi saboda nauyin da aka ɗora musu za a samu matan sun zama kamar maza wajen neman abin duniya.

Babu sana’ar da matan nan ba sa bugawa a ƙoƙarinsu na sama wa iyalinsu abin kaiwa bakin salati da na gudanar da rayuwar yau da gobe.

Irin wannan yanayi ya jefa mata da yawa cikin harƙallar cin bashi inda wasu da yawa suke gurfana a kotuna yayin da wasu ma suke ɗaure a kurkuku saboda bashin da ke kansu.

Wasu matan kuwa sukan bi gidajen masu hali suna wanke-wanke ko wanki da sauran ayyukan gida ne don kula da iyalansu.

A gidan da irinsu ke aiki ne za su ɗan samo abinci da ƙanzon da suka yi wanke-wanke su taho da shi gida don iyalinsu.

Haka ɗan kuɗin aikin za a tarar bai taka kara ya karya ba, amma da shi ne za a yi ta gudanar da rayuwar yau da kullum saboda mazan sun bar musu nauyin gidan a kansu.

Har ila yau irin wannan yanayi ya jefa wasu matan da dama ga yin bara da maula. Irin wadannan mata ba sai a gidaje ko kasuwanni za ka tarar suna yawon bara ba, har ma a kan tituna da wuraren taruwar jama’a.

Ga duk mai bin titunan biranen kasar nan zai ga yadda irin wadannan mata ke yini a rana su da ƙananan ’ya’yansu wani lokaci ma har da goyo.

Za ka ga suna bin motocin da ke titi suna yin bara ba tare da tunanin haɗarin da hakan ka iya jefa rayuwarsu a ciki ba.

Irin wannan sakar wa mata nauyin gida da maza suke yi ya janyo a yanzu mazan suka rasa ƙima da daraja a gidajensu.

Za a tarar a irin wannan yanayi mjin ba ya da kartabus. Idan ya bayar da umarni ba a bi, haka idan ya yi hani ba a hanuwa.

Wata matar aure a Kano, mai suna Hajiya Fatima Yahaya ta bayyana wa Aminiya cewa yanayin da mata ke ciki na ɗaukar nauyin gida ba gata aka yi wa matan ba, domin an ɗora musu abin da ya fi ƙarfinsu ne.

“Su matan da suke ganin kamar wani abu ne na burgewa gare su na su gudanar da harkokin gida, a gaskiya a ganina ba gata aka yi musu ba.

“Domin wallahi ko ba za ki ba da kudinki a cika ba, to wannan zirga-zirgar da za ki yi ba karamin abu ba ne, domi ba ki samun natsuwar da ta dace.

“Tun da nake ban taba sha’awar a ce miji ya sakr wa matarsa harkar gida a hannuntta ba,” in ji ta.

Ita ma Hajiya Jamila Adamu ta ce halin da mata suke ciki na sakar musu nauin gida abin da tausaya musu ne.

Ta ce, “Abin nan fa sai dai mu ce ‘Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.’ An bar wa mata nauiyn da Allah bai dora musu ba.

“Mata da yawa sun firgice ba su cikin hayyacinsu. Ita mace a ka’ida halittarta ba ta jure wahala. A yanzu ta kai wani namijin yana kwance a gida matarsa za ta fita ta je kanti a unguwa ta sayo kayayyaki ta kuma dawo gida.

“Kai wani ma shi zai aiki matar tasa kanti don sayo masa wani abin amfani. Wannan lalacewa da me ta yi kama? Na rasa abin da yake damun maza a wannan zamani.”

Ta yi kira da maza su ji tsoron Allah su tsaya tsayin-dakasu sauke nauyin da Allah Ya dora msuu hakan ne kadai zai kai al’umma tudun-mun-tsira.

Wani magidanci, Malam Ibrahim Liman, ya bayyana wa Aminiya ceaw rashin sanin darajar kai ne ya sa maza suke bar wa mata nauyyin kula da gida.

“Idan namiji  ya san kimar kansa wallahi ba zai yarda matarsa ta dauki nauyin kula da kanta ba, ballantana ’ya’yansa ba,” in ji shi.

Gazawa ce ga maza —Malamin Musulunci

Ustaz Ali Dan Abba malamin addinin Musulunci ne a Kano ya bayyana wa Aminiya cewa duk naimjin da ya auri mace ya bar ta da nauyin kula da gida to ya zama gajiyayye, ya rasa kimar da Allah Ya halicce shi a kantta.

“A shari’ance miji shi yake sakar musu nauyin iyalinsa amma idan aka wayi gari mace ce za ta yi komai a gidan to wannan mazagazawa ce ga mijin.

“Haka kuma zai kasance ba zai samu biyayyar matar a gare shi ba.

“Allah Yana cewa “Maza su ne tsayayyu a kan mata saboda abin da suke ciyarwa daga dukiyoyinsu.”

Haka Allah Ya ce “Wanda aka haifa wa, wato uba ke nan to ciyarwa da shayarwa suna kansa.”

Malamin ya ce idan har maigida ya jajirce ya yi kokarin ciyar da iyalinsa, Allah zai taimake shi ba zai rasa abin da zai ciyar ba.

Don haka ya yi kira ga maza su ji tsoron Allah su dauki nauyin iyalinsu kamar yadda Allah Ya dora musu.

“Ya kamata maza su tashi su nemi na kansu, mutum ko karamar sana’a yake yi Allah Zai taimake shi a wannan sana’a ko da ciyawa yake yi yake sayarwa, zai samu abin da zai ciyar da iyalinsa daidai karfinsa.

“Amma ba abu ne mai kyau mutum ya zauna ya ce wai ba ya da sana’ar da zai dauki nauyin iyalinsa, wannan ba dalili ba ne,” in ji malamin.