✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda motar da Kwankwaso ya ba ni ta taimaka min na tsira daga harin Boko Haram —Buhari

Kwankwaso ya taka rawar tseratar da ni daga harin bam da aka kai min a shekarar 2014.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake yin tsokaci kan yadda tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya taka rawar tseratar da shi daga harin Boko Haram da aka kai masa a shekarar 2014.

A wata tattaunawa ta musamman da Gidan Talabijin na Trust TV, Shugaba Buhari ya bayyana yadda aka kai wa tawagar motocinsa hari a Jihar Kaduna, shekara guda kafin karbar mulki a hannun tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan.

A wancan lokaci dai, Shugaba Buhari ya tsallake rijiya da baya a Kasuwar Kawo da ke birnin na Kaduna, sai dai uku daga cikin dogarawansa sun jikkata da har ta kai su ga kwanciya a gadon asibiti.

A lokacin da aka kai harin, wani hadimin shugaban kasar ya ce dan kunar bakin waken da ke cikin wata mota kirar Toyota Sienna, ya kutsa cikin ayarin motocin Buhari inda ya tayar da bam din da ke dauke da shi.

Babu shakka Buhari ya tsallake rijiya da baya, amma motarsa, wata kirar Toyota Land Cruiser da wadda ke bayanta sun fuskanci mummumar barna sanadiyar harin.

Hoton motar bayan aukuwar harin

A cikin wani shirin na musamman mai taken, ‘Muhimmacin Muhammadu Buhari’, Shugaban Kasar ya ce motar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ba shi ce ta taimaka masa ya tsira daga harin.

“Lallai wannan karamci ne daga Kwankwaso. Shi ya ba ni wannan mota ya ce na yi amfani da ita saboda kujerar da nake nema ba karama ba ce don haka ba zan rasa masu zafin adawa da za su nemi kawar da ni daga doron kasa ba.

“A lokacin zan kai ziyara Kano daga Kaduna a cikin motar kirar jeep, sai wata mota ta yi kokarin ketare mu amma ’yan rakiyata suka hana ta, kwatsam sai ta kutsa cikin daya daga cikin motocin kuma nan da nan bam ya tashi.

“Da na leka, sai na hangi sassan jikin mutane wasu sun yi gunduwa-gunduwa saboda yadda bam din ya tarwatsa su. Amma babu daya daga cikin mu da ya samu rauni a cikin motar.

“Sai dai ban san ta yaya na ga jini a jikin tufafi na ba saboda yawan mutanen da bam ya kashe a waje,” inji Buhari.

Kuna iya kallon cikakken shirin a kafar Trust TV, a tashar Channel 164 da ke Star Times da karfe 6 na yammacin ranar Talata.