✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muka kwana a daji — Daliban GSSS Kankara

’Yan bindigar sun rika kiran mu da mu dawo tare da cewa babu abin da zai same mu.

A daren jiya na Juma’a ne wasu ’yan bindiga suka kai hari a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati (GSSS) da ke Kankara, Jihar Katsina.

Wasu daga cikin daliban da suka kwana a dajin inda suka gudu don neman mafaka sun dawo a safiyar Asabar, yayin da wasu kuma da ke cikin wadanda ’yan bindigar suka tattara an tsinto su bayan an bi sahun maharan.

Wani dalibin aji hudu, Kabir Isah, daya cikin wadanda suka kwana a dajin, ya labarta wa Aminiya irin wahalar da ya sha da yadda ta kasance ga sauran ’yan uwansa dalibai.

“Mun baro ajujuwa bayan mun tashi daga karatun dare da misalin karfe 9.00 na dare kuma muka koma dakunanmu na kwana.”

“Da misalin karfe 10.30 yayin da wasunmu tuni sun kwanta, kawai sai muka fara jin harbin bindiga, sai ga manyan dalibai sun rugo suna tashin mutane.”

“A yayin da wasu daga cikinsu ke cewa ya kamata mu gudu don neman tsira, wasunsu kuma na cewa kamata ya yi mu taru a dakunan kwanan mu fara fahimtar lamarin tukunna kafin daukar mataki na gaba.”

“Yayin da muka ji harbe-harben na kara matsowa kusa, sai muka tunkari katangar makarantar muka tsallaka cikin daji.”

“Daga nan ne sai ’yan bindigar suka fara kiran mu cewa babu abin da zai same mu, amma daga karshe sun karbi kudi da wayoyi a hannun wadanda suka makale a makarantar.”

“Mun yi gudu na kimanin awanni uku a cikin dajin, kafin muka taru a wani wuri karkashin bishiyoyi muka zauna a farke har sai lokacin da muka fara jin kiran sallar Asuba.”

“Yawancinmu mun samu raunuka yayin tsallake katangar da kuma lokacin da muke gudu a cikin daji, amma mun gode wa Allah mun dawo gida sai dai mun samu labarin cewa maharan sun yi awon gaba da wasu daga daliban,” inji shi.

Isa ya ce kaninsa dan aji daya a makarantar, har ya zuwa lokacin da ya zanta da Aminiya bai dawo ba.

Ya yi addu’ar Allah ya shiga lamarin domin dawo da zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya, tare da yin kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da rubanya kokarinsu na magance matsalolin tsaro a kasar.