✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mutumin da ake tuhuma da kashe Hanifa ya gurfana a Kotu

Za a yanke hukuncin a wannan shari’ar cikin watanni biyu babu makawa.

Abdulmalik Muhammad Tanko, malamin makarantar da ake tukuma da garkuwa da kuma kashe dalibarsa ’yar shekara 5 Hanifa Abubakar ya bayyana a gaban kotu karon farko a ranar Litinin.

Aminiya ta ruwaito cewa, Abdulmalik ya bayyana gaban kotun ne tare da mutane biyu, Hashimu Ishiyaku, da Fatima Jibrin Musa da ake zargi suna da hannu a garkuwa da kuma mutuwar Hanifa.

Bayan sauraron karar, Lauyan gwamnati kuma Mai shari’ah Muhammad Lawan ya dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga watan Fabrairun wannan shekara domin ba lauyoyin gwamnati da za su kare Abdulmalik damar gudanar da nasu binciken.

Kotun tana tuhumar mutanen uku da laifuka da suka hada da hada baki, garkuwa, boyewa da kuma ajiye yarinyar da suka yi garkuwa da ita a wuri daya, da kuma kisan kai, laifukan da suka amsa aikatawa.

A kan haka ne Kotun ta Majistare mai lamba 12 da ke Gidan Murtala a Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare wadanda ake tuhumar da kisan Hanifa a gidan gyaran hali har na tsawon mako biyu.

Da yake tsokaci a kan batun, Babban Lauyan Gwamnatin kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Musa Abdullahi Lawan, ya ba ’yan Najeriya tabbacin cewa, za a yanke hukuncin a wannan shari’ar cikin watanni biyu babu makawa.

A cewar Barista M A. Lawan, “ina so in tabbatar maku cewa, Ma’aikatar Shari’a za ta shigar da kara a kotun da ya kamata cikin kwanaki uku zuwa hudu masu zuwa.

“Za mu bi batun sau da kafa, kuma a cikin wata daya ko biyu masu zuwa za mu kamala maganar wannan karar,” inji Barista Musa.

Aminiya ta ruwaito Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yana cewa a shirye yake ya sa hannu a aiwatar da hukuncin kisa a kan wanda ake zargi da kisan Hanifa muddin kotu ta yanke masa hukuncin.

Ganduje ya sha alwashin cewa ba zai yi wata-wata ba wajen sanya hannu a zartar masa da hukuncin da kotu ta yanke da zarar an kai teburinsa.

Ya bayyana hakan ne ranar Litinin, lokacin da ya jagoranci tawagar Gwamnati da ta Majalisar Dokokin Jihar zuwa gidan su Hanifa da ke unguwar Dakata/Kawaji a birnin Kano.

A zartar wa wanda ya kashe Hanifa hukuncin kisa a bainar jama’a —Aisha Buhari

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta bayyana goyon baya a kan kiraye-kirayen da ake yi na zartar da hukuncin kisa a bainar jama’a ga mutumin nan da ake zargi da kashe dalibar ’yar shekara biyar a Jihar Kano.

Cikin wani bidiyo da a yanzu ya karade dandalan sada zumunta, wani fitaccen malamin addinin Islama a Kano, Malam Abdallah Gadon Kaya, a daya daga cikin karatuttukansa ya yi kira da a zartar da hukuncin kisa a bainar jama’a kan Abdulmalik Tanko ta irin hanyar da ya kashe dalibar tasa Hanifa.

Malam Abdallah ya yi da’awar cewa, a kashe mutumin a bainar jama’a domin hakan zai zama izina ga kowa, lamarin da ya ce umarni kawai Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano za su bayar kuma aikin gama ya gama.

Ita ma uwargidan shugaban kasar ta wallafa wannan bidiyo na Malam Abdallah a shafinta na Instagram, inda ta bayyana goyon baya dari bisa dari a kan wannan kira.

A sakon da Aisha ta wallafa, ta ce “muna goyon bayan da’awar da Malam ya yi.”

Kisan Hanifa dabbanci da rashin imani ne —Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana takaicinsa bisa kisan Abdulmalik da sauran wadanda ake tuhuma suka yi wa Hanifa.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a makon jiya, Atiku ya kwatanta lamarin a matsayin “mummunan labari.”

“InnalilLahi wa inna ilayHi raji’un. Na samu mummunan labarin kisan gilla ga yarinya Hanifa ’yar shekaru 5, wadda aka kashe bayan kwashe kwanaki 47 a hannun masu garkuwa.

“Wannan dabbanci da rashin imani ne. Na kasa fahimtar yadda mutum mai hankali zai raba yarinya karama da iyayenta sannan daga bisani kuma ya kashe ta,” a cewar sakon da Atiku a wallafa a shafinsa na Facebook.

Atiku ya kuma mika sakon jajensa tare da yin ta’aziyya ga iyalan Hanifa yana mai kira da a bi mata kadinta.

“Ina kira ga mahukunta da su tabbatar (masu garkuwar) sun fuskanci hukunci.”

Matasa sun kone makarantar da aka binne Hanifa

Wasu fusatattun matasa sun kone Makarantar Noble Kids Academy da ke Jihar Kano biyo bayan sacewa da kuma kashe yarinyar nan mai shekaru biyar, Hanifa Abubakar da malaminsu ya yi.

Wani bidiyo da wakilinmu ya nado ya nuna yadda aka cinna wa makarantar wuta da misalin karfe 1 na daren Lahadi wayewar garin Litinin.

A yayin da dubban mutane ke ta tofin Allah-tsine da bayyana takaicinsu kan wannan lamari, shi ma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin cewa a tabbatar an yi adalci wajen neman hakkin yarinyar da aka kashe bata ji ba bata gani ba.

Matashiya: ‘Da shinkafar bera ta N100 na yi amfani wajen kisan Hanifa’

Abdulmalik Tanko, malamin makarantar da ake zargi da kisan Hanifa, ya ce da shinkafar bera ta N100 ya yi amfani wajen kasheta.

Wanda ake zargin dai shi ne mai makarantar Noble Kids da ke Kano, kuma ya kashe yarinyar ne bayan ya sace ta, sannan ya yi yunkurin karbar kudin fansa daga iyayenta.

Tun farkon watan Disamban bara ne aka sace Hanifa lokacin da take kan hanyar komawa gida daga makarantar Islamiyya.

Malamin dai ya bukaci a biya shi Naira miliyan shida a matsayin kudin fansarta, inda a wajen karbar kudin ne dubunsa ta cika.

Sai dai ko a lokacin da yake kokarin karbar kudin fansar ma ya riga ya hallaka ta, amma ya ki shaida wa iyayenta.

To sai dai bayan kama shi, wanda ake zargin ya shaida wa ’yan jarida a hedkwatar ’yan sandan Kano ranar Juma’a cewa da shinkafar bera na N100 ya yi amfani wajen kashe yarinyar.