Daily Trust Aminiya - Yadda na tsere daga hannun masu garkuwa —Abubakar

Yadda na tsere daga hannun masu garkuwa —Abubakar

Tun bayan kama masu yi wa masu garkuwa da mutane leken asiri su biyar da aka yi a garin Zariya a kwanakin baya, ba a sake kai hari ba sai a daren Litinin din nan.

Wani wanda ya kubuto daga hannun masu garkuwa da mutane, Abubakar Adamu,  ya bayyana wa Aminiya abin da ya faru da shi a lokacin da ’yan bindiga suka tasa su suna korawa kamar shanu.

Ya ce sun yi tafiya mai tsawo, tun daga Zariya sai da suka bullo ta garin Rigacikum da ke wajen garin Kaduna.

Ya ce a daren na Litinin din ne masu satar mutane don neman kudin fansa suka kwashe su su takwas a kauyen Garungo da ke yankin Kofar Gayan a Karamar Hukumar Zariya.

Daya daga cikin wadanda aka dauka amma Allah Ya kubutar da shi, ya tsere bayan sun yi tafiya mai nisan gaske ya shaida wa wakilinmu cewa a cikin daren sun ji harbe-harben bindiga.

– ‘Yadda aka shiga gidanmu’

“Kafin ka ce wani abu sai muka ji an fara buga gidan da suna cewa in bude gidan, sai na ce ba zan bude ba don ban san ko su wane ne ba.

“Sai suka ce su Abba ne sai na ce wane Abba? Suka ce baki ne zan sa su a hanya,” inji shi.

Daga nan sai ya ce musu shi ma bako ne, “Sai suka ce in bude, in ba haka ba zu su balle, kuma in suka shigo za su kashe mutanen da suke cikin gidan.”

Ya ci gaba da bayanin cewa, “’Yan bindigar su goma sha daya ne kuma sun yi tafiya mai nisa sosai a kafa.”

Malam Abubakar Adamu ya ce a gidanshi mutum biyar aka tafi da su, “Sai kuma a kan hanyarmu sun kara kama mutum uku.”

– Yadda na kubuta

A game da yadda ya samu kubuta daga hannunsu kuwa, ya ce sun karyo masara ne sai suka zabe shi da wani, “Suka ce mu je mu karyo itace”.

Sai, ya ce wa dayan ya zo su tafi sai su yi amfani da damar su tsere, amma ya ce in suka gane za su kashe su kamar yadda suke furta musu.

Ya ce yana cikin karyar itacen sai ya fahimci cewa hankalinsu ba ya akan sa sai ya taki sa’a na gudu.

Karin Labarai