✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rashin haihuwa ke kawo mutuwar aure

Likitoci da malaman Musulunci sun bayyana rashin haihuwa a matsayin daya daga cikin manyan dalilan mutuwar aure

Likitoci da malaman Musulunci sun bayyana rashin haihuwa a matsayin daya daga cikin manyan dalilin da ke haddasa mutuwar aure a cikin al’umma.

Sun alakanta rashin haihuwa a matsayin tushen yawancin rikice-rikicen da ke tsakanin ma’aurata da a karshe suke kaiwa ga mutuwar auren.

Wani kwararren likitan mata a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Obafemi Owolowo, Farfesa Ajenifuja Olusegun, ya yi kira da a daina alakanta matsalar rashin haihuwa da mata kadai.

Ya bayyana cewa duk da cewa mata ne ke daukar juna biyu, amma matsalar rashin haihuwa na iya kasancewa daga bangaren na miji, don haka ba matsala ba ce da ta kebanci wani jinsi.

A jawabinsa ga taron da kungiyar Musulunci ta Standar Bearers ta shirya kan matsalar rashin haihuwa, masanin ya ce maimakon dora wa juna laifi, abin da ya kamata shi ne ma’aurata su rika samun cikakken ilimi kan abubuwan da suka danganci matsalar ta rashin haihuwa da kuma neman magani.

Farfesa Ajenifuja Olusegun, ya ce daga cikin hanyoyin samun mafita daga matsalar rashin haihuwa, ma’aurata na iya tunutubar kwararrun malamai.

Malami ma Jami’ar Al-Hikmah University, da ke Ilorin a Jihar Kwara State, Dokta Nafiu Al-Jawhari, ya bayyana cewa amfanin haihuwar ’ya’ya ba abu ne da ta kebanci rayuwar duniya ba, domin har bayan rayuwa, iyaye sukan amfana da ’ya’yansu.

Shugaban kungiyar Musulunci ta Standard Bearers, Dokta Nurudeen Abdulraheem, ya ce an shirya taron ne domin wayar da kan Musulmi kan ka’idojin addinin wajen amfani da magungunan zamani.