✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rufe gidajen wasan kwaikwayo ya rage barna a Zariya

Mazauna sun yi na'am da rufe gidajen karuwai da na damben gargajiya

Miyagun laifuka sun ragu sakamakon rufe gidajen giya da gidajen karuwai da na damben gargajiya da na wasan kwaikwayo a Karamar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna.

Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari, Muhammad Usman ya ce mazauna yankin sun nuna gamsuwa da matakin da suka ce ya takaita ayyukan barna a yankin.

Shugaban Karamar Hukumar ya ce Karamar Hukumar ta rufe gidajen badalan ne domin aiwatar da dokarta ta hana ta’ammuli da kayan barasa wanda ya yi tasiri wurin a rage miyagun laifuka.

Ya kara da cewa mazauna sun yi na’am da dokar wadda ta kuma takaita adanawa da kuma dillancin kayan barasa.

Alhaji Muhammad Usman ya ce dama can masu gidajen giyan na gudanar da harkokinsu ne a haramce a Karamar Hukumar, kuma sun bijire su nemi izinin gudanar da harkokinsu.

“Mun kira masu kayan barasa a Sabon Gari muka bayyana musu cewa dole sai sun samu lasisi kafin su gudanar da harkokinsu a yankin kamar yadda dokar ta tanada.

“Sun yi watsi da mu, suka kuma shigar da kara a Babbar Kotun Jihar Kaduna.

“Bayan Kotun da ke zamanta a Dogarawa ta yi watsi da karar sai Karamar Hukumar ta shigar da karar neman izinin rufe gidajen giyan saboda ba su lasisi.

“Batun na gabar Babbar Kotun Majistare da ke zamanta a Sabon Gari’’, kamar yadda ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).

Shugaban Karamar Hukumar ya bayyana cewar ba da nufin kuntata wa kowa ba aka kafa dokar.