✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sana’ar sarrafa fatar dabbobi ta samu karbuwa a Kamaru

Fatun wasu dabbobi kamar shanu  da tumaki da kuma rakuma da ake yankawa domin sayar da namansu, ana  amfani da su wurin samar da wasu…

Fatun wasu dabbobi kamar shanu  da tumaki da kuma rakuma da ake yankawa domin sayar da namansu, ana  amfani da su wurin samar da wasu abubuwan amfani bayan an sarrafasu.
Ana iya samar da takalma, huluna, warwaro da sauransu daga fatar rago misali idan aka jeme. Baya ga wadannan kuma akwai tarin abubuwa  daban kamar kayan kawata gida. Irin wannan sana’ar  ta fi yawa a arewacin kasar Kamaru, inda aka ware wurin guda domin tallatar da irin wadannan kayayyaki.
Abin da yake kawo baki masu yawon bude ido da kuma sayan wadannan kayayyakin da suke tafiya da su zuwa kasashen ketare. Kodayake, yanzu haka sana’ar da kuma kasuwancin suna fuskantar  wasu matsaloli a dalilin rashin tsaro da yake addabar lardin Arewa-mai-Nisa.
Sana’ar jima ta kunshi jama’a da dama da suka fito daga sassa daban-daban. Akwai wadanda gado suka yi, wasu kuma koyon sana’ar suka yi wato haye suka yi, a yayin da wani kaso kuma makwabtaka ne da masu yin jima ya sa suka kwadaita da shiga wannan sana’ar.
Gabannin sarrafa abin da ake so, bayan ana da fatu, da farko dai ana tafiya rafi, ko kuma gulbi a jika fatu a cikin isasshen ruwa, bayan ya jika sosai sai a wanke da garin sabulu, da kuma wani sinadari mai kawar da kwayoyin cuta, ya kuma fidda dauda da kuma jini, daga bisani kuma sai a dauraye. Bayan an gama daurayewa ne, sai a tsoma fatar.
 Daga nan ana bukatar samun toka da kuma farar kasa da ake shafawa a bangon dakuna  hadi da kashin tsuntsaye da za a barbada akan fatar domin hakan ya sawaka kawar da gashin da yake jikin fatar, tsumin kuma na bukatar  kwanaki uku gabannin a fara kankare fatar a kawar da duka gashin jikin fatar.
Idan aka gama wannan matakin, sai a yi kokarin mikar da fatar ana bugawa domin ta yi laushi. Wasu suna ajiye gashi da aka cire domin su yi darduma da shi ko kuma su kawata wasu kayayyaki daban da za su kera nan gaba.
Wani mai sana’ar kankare fatu ya ce akwai rufin asiri sosai albarkacin wannan sana’a. A yini guda mutum na samun akalla CFA 50,000 kwatankwacin Naira 17,000. Saboda da haka suke samun damar hada wa da sana’ar noma da kiwo a kan jima. Sai dai ya koka kan wani batu, inda ya ce masu yawon bude ido, wadanda sune suka fi yi musu ciniki ba su shiga yankinsu a yanzu haka sanadiyyar tabarbarewar tsaro.
Sai dai a wasu lokuta wasu manyan ’yan kasuwa daga kasashen Gabon da Burkina Faso suna  yin odar fatun daga Kamaru.