✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda sauran masu sallar Tahajjud 10 da aka sace a Katsina suka kubuta

Ko tafiyar da aka yi da mu ai azaba ce balle kuma ace ga dauri.

Rahotanni daga Jihar Katsina sun bayyana cewa, ragowar mutum goma da ’yan bindiga suka sace a Karamar Hukumar Jibiya yayin da suke sallar Tahajjud sun kubuta.

Aminiya ta ruwaito cewa, an kubutar da mutum 30 daga cikin mutum 40 da ’yan bindiga suka yi gakuwa da su a yayin da suke yin sallar Tahajjud a wani masallaci da ke Unguwar Kwata a Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Gambo Isah, ya ce, “Sun tafi da mutum 40, amma Allah cikin ikonSa lokacin da muka samu labari, ba tare da bata lokaci ba, jami’an tsaron suka bi sawun maharan kuma an yi nasarar ceto mutum 30 a lokacin.”

Sai dai ya ce akwai mutum 10 da ba a san inda suke ba, amma babu tabbacin ko suna hannun ’yan bindigar.

Yadda ragowar mutum goman suka kubuta

Kamar yadda majiyarmu ta bayyana, daga cikin wadannan mutane 10 da aka tafi da su, wasunsu sun samu tserewa tun kafin a kai inda za a ajiye su, inda a karshe mutane biyar suka rage a hannun su, ciki har da mai karamin yaron.

A cewarta, “A ranar Talatar nan Allah Ya kaddari sake kubutar sauran biyar da amma an baro mai goyon a can.

“Daga cikin wadanda suka kubuta har da wata budurwa.

“Kwatsam, sai kuma ga ita wannan mai goyo Allah Ya kubutar da ita a inda ta fito daga cikin dajin da aka boye su zuwa bakin titi a safiyar yau Alhamis a garin Gurbi ta Jihar Zamfara.

Kamar yadda muka ji daga bakin daya daga cikin wadanda suka kubutan wacce ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce “matar daya daga cikin barayin da suka sace mu ce ta kwance mu don mu gudu.

“Ta bamu labarin cewa, auren tilas aka yi mata da barawon da take zaune da shi a yanzu, saboda kashe mata mijin farko da aka yi ya sa aka tilasta mata auren wannan.

“Mun dai baro ta bamu san abin da zai faru da ita ba, sannan batun shan wuya ai ba sai an fada ba.

“Ko tafiyar da aka yi da mu ai azaba ce balle kuma ace ga dauri.

Ya zuwa yanzu dai rundunar ’yan sandan Jihar ta ce tana ci gaba da bincike a kan lamarin kamar yadda Kakakinta SP Gambo ya sanar.

Masallacin da aka sace mutum 40 a unguwar Kwata (Abatuwa) da ke Jibiya.

Yadda aka sace masu sallar Tahajjud 

’Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kutsa masallacin ne da tsakar dare, suka yi awon gaba da mutum 40 daga cikin masu sallar Tahajjud kafin wayewar garin Litinin.

Maharan sun yi wa masallacin dirar mikiya ne da misalin karfe biyu na dare, inda da farko suka yi awon ga da masallata 47, amma bakwai daga ciki suka tsere daga hannunsu.

Wani mazaunin garin, Lawal Jibiya, ya ce mazauna kauyukan da ke makwabtaka da su sun ankarar da su a kan yunkurin kawo harin na ’yan daban daji.

A kan haka ne daruruwan matasa da ’yan sa-kai suka yi shiri da jihan maharan a hanyar shiga garin ta Daddara, Kukar Babangida da Magama.

Sai dai ya ce sun yi rashin sa’a saboda maharan sun sauya hanya suka biyo ta kusa da Asibitin Yunusa Dantauri.

Ya kara da cewa, ’yan bindiga ba su yi harbi ko sau daya ba har sai da suka gama tattare masallatan suka kama gabansu.

SP Gambo ya ce, “Sabon masallaci yana nan a kan hanyar zuwa Madatsar ruwa ta Jibiya, inda akwai karancin zirga zirgar mutane wanda hakan ne ya bai wa ’yan bindigar damar kawo wannan hari.”