Yadda sayar da kuri’a ke barazana ga dimokuradiyyar Najeriya | Aminiya

Yadda sayar da kuri’a ke barazana ga dimokuradiyyar Najeriya

Wani mutum yayin da ya ke kada kuri’a a Zaben 2019
Wani mutum yayin da ya ke kada kuri’a a Zaben 2019
    Abiodun Alade da Dalhatu Liman

A shekarun baya zabe a Najeriya yana cike da sace akwatin zabe ne da ta da zaune-tasye da aringizon sakamakon zabe, sai dai bayyanar fasahar zamani tare da inganta tsaron zabubbukan sun sa ’yan siyasa da jam’iyyun siyasar sun bullo da sabuwar hanya ta sayen kuri’u don samun nasara a zabubbukan.

Yayin da fiye da ’yan Najeriya miliyan 80 ke rayuwa a cikin bakin talauci (samun kasa da Naira 800 a rana) kamar yadda Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta nuna.

Ba abin mamaki ba ne idan ’yan siyasa suka rika jan hankalin masu zabe da abin da bai taka kara ya karya ba kamar kofunan shinkafa da wake da gari da sauran kayan abinci ko kuma wasu kananan kyautuka a lokutan kamfe.

Yayin da a wasu lokuta kuma, suke amfani da dan kudin da bai wuce Naira 500 ba suna rabawa a ranar zabe.

Lamarin yana faruwa ne a kusan dukkan jihohin kasar nan, amma ya kara fitowa fili ne a zabubbukan Gwamna da aka gudanar a jihohin Ekiti da Osun a kwanan nan.

An zargi wakilan jam’iyyu da sayen kuri’u a farashin da bai wuce Naira 2,000 ba a yayin zaben Gwamnan Jihar Osun, wanda ya kasance zaben da daga shi sai babban zaben 2023.

A wasu rumfunan zabe, an ga wakilai da magoya bayan jam’iyyu suna rige-rigen shawo kan masu zabe da alkawuran kudade.

Daya daga cikin dabarun da suka yi amfani da shi, shi ne bai wa mai kada kuri’a wata takarda ko lambobi domin hakikance kudirinsa a ranar zaben.

Sai dai jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) sun kama wadansu mutane bisa zargin samun su da hannu a sayen kuri’u yayin zaben.

Daga cikin wadanda suka shiga komar hukumar akwai Yekini Nurudeen Abiodun, bisa zargin sayen kuri’u a Rumfa ta 002 a Mazaba ta 08, a yankin Isale Agbara na Karamar Hukumar Osogbo da Jimoh Kazeem da Adeyemo Bahir da Abidogun Ismail – da aka kama su a Rumfa ta 002, Mazaba ta 2, a yankin Ababu na Karamar Hukumar Isale Osun.

Yadda ake sayen kuri’un

Wata kungiya mai sa ido a kan zabe, mai suna YIAGA Africa, wacce ta tura jami’ai 500 zuwa rumfunan zabe masu zagayawa 32 don sa-ido, a karkashin tsarinta da ta yi wa lakabi da sa-ido a kan kuri’a, (Watching The Vote -WTV), a dukkan kananan hukumomi 30 da ke Jihar Osun-a rahoton da ta fitar ta ce wakilan manyan jam’iyyun siyasar kasar nan biyu – APC da PDP sun sayi kuri’u.

Rahoton wanda Shugaban Kungiyar, Dokta Hussain Abdu da Babban Daraktan Kungiyar, Samson Itodo, suka rattaba wa hannu sun ce wakilan jam’iyyun sun sayi kuri’un a kan Naira 2,000 a wasu wuraren.

“Kungiyar Yiaga Africa ta samu gamsassun bayanan da suka tabbatar da wakilan jam’iyyun APC da PDP sun sayi kuri’u a wasu rumfunan zaben.

“Misali a rumfa ta 009, da ke Makarantar Akinlalu Commercial Grammar School, Mazaba ta 01 a Karamar Hukumar Ife ta Arewa, wakilan jam’iyyun sun samu waje suka fake a kusa da tantin kada kuri’a domin tabbatar da yadda masu zaben suke dangwala wa jam’iyyun nasu.

“A Rumfa ta 003 daura da Kasuwar Olomu a Osogbo, an ga wakilan Jam’iyyar PDP suna bai wa masu kada kuri’a daga Naira 2000 zuwa 5000 domin shawo kansu.

“Har wa yau, a Rumfa ta 003, Mazaba ta 007 a Karamar Hukumar Orolu, an ga yadda wakilan Jam’iyyar APC suke bai wa kowane mai kada kuri’a Naira 4,000 bayan sun dangwala wa jam’iyyar yayin da aka ga wakilan Jam’iyyar PDP a daya bangaren suna rarraba wa masu kada kuri’a Naira 2, 000 domin samun kansu,” inji rahoton.

Hakazalika, jagorar wata kungiya mai rajin tsarkake harkokin zabe da ta sa ido a zaben na Osun, mai suna CLEEN Foundation, Misis Chigozirim Okoro, ta ce an hadu da yawaitar sayen kuri’u a yayin zaben na Osun.

Kungiyar ta ce jami’an tsaron da suka aiki a zaben sun yi ko oho yayin da wakilan jam’iyyun ke rige-rigen sayen kuri’un a filin Allah.

Ta ce, “Misali a Rumfa ta 014, Mazaba ta 05, da ke wurin wasanni na Jami’ar Obafemi Awolowo, a Karamar Hukumar Ife ta Tsakiya, an ga yadda dan wata jam’iyya yake alwashin zai ba da Naira dubu 10 ga wanda yake shirye ya zabi jam’iyyarsa.

“Har ila yau a Rumfa ta 009, Mazaba ta 11, da ke yankin Oke Aree a Karamar Hukumar Boripe an ga yadda aka yi ta dillancin kuri’u na fitar hankali inda ake bukatar mai zabe ya nuna shaidar ya zabi jam’iyya sannan sai wakilan jam’iyyun su mika masa shaidar ya yi hakan domin ya je ya karbi kasonsa.

A Rumfa ta 09 Mazaba ta 01, a yankin Idilapo Ogodobo da ke Karamar Hukumar Obokun an ga yadda ake raba wa masu kada kuri’a kudi a wata mashaya don su zabi wata jam’iyya.

“Sannan an yi wa wadansu alkawuran abinci bayan sun dangwala kuri’unsu.

Dadin dadawa, a Rumfa ta 14, Mazaba ta 05 da ke cikin Jami’ar Obafemi Awolowo an ga yadda masu kada kuri’a suke rubuta sunayensu ga wata jam’iyya domin karbar Naira 3, 000 zuwa dubu 10 daga wasu jam’iyyu.

Sannan a Rumfa ta 009, Mazaba ta 11 a yankin Oke Aree, Karamar Hukumar Boripe, wakilan jam’iyyun sukan kutsa cikin tantin dangwala kuri’a don tabbatar da hakikanin jam’iyyar da mai kada kuri’a ya zaba,” inji ta.

An yi amfani da lambobi da tikiti don karbar kudi

Wacce ta kafa Gamayyar Kungiyoyin Fararen Hula, Misis Ene Obi, ta ce yayin da suke sa-ido a zaben, sun gano wasu dabarun sayen kuri’un, ta hanyar amfani da lambobi da wasu takardu da aka sa wa hannu don tabbatar da kudirin masu kada kuri’a.

Aminiya ta gano yadda a wasu rumfunan zabe, wakilan jam’iyyu suka rika bai wa masu kada kuri’a lambobi da tikiti bayan sun tabbatar da sun dangwala wa jam’iyyunsu.

Daga nan sai mai kada kuri’ar ya je da lambobin ko tikitin ga mutumin da ke raba kudin, wanda ke boye a gida na uku zuwa hudu daga rumfar zaben ko a cikin aji, idan rumfar zaben ta tana harabar makaranta ce.

Sai dai an samu wasu daidaikun misalai inda masu kada kuri’ar suka zabi abin da ransu ke so duk da sun karbi kudi daga wakilan wata jam’iyya.

‘Dalilin da muke sayar da kuri’unmu’

Wadansu masu kada kuri’a sun ce bakin talaucin da ake fama da shi a Najeriya ne ya tilasta musu sayar da kuri’unsu, musamman idan aka yi la’akari da hauhawar farashin kaya da rashin aikin yi a yanzu.

Wani mai suna Kunle Ahmed, ya ce an nemi ya sayar da kuri’arsa a kan Naira dubu 10, kuma ya sayar. “Ina zaman kashe wando a tsawon lokaci.

“Yaya zan ci abinci ke nan? Kana jin kuri’ata za ta iya hana wanda zai lashe zaben samun nasara?

“Kuri’a daya ce tal kuma idan ma ban karbi kudin ba, wani zai karba,” inji shi.

A cewar Misis Abimbola Ogundele wadansu masu kada kuri’ar sun yi amanna cewa kudaden da ’yan siyasar suke rabawa dama na talakawa ne saboda haka ba su wata damuwar karbar kudaden.

Wata da yanzu ta fara kada kuri’a, Afolabi Waliat Adesewa, ta ce ta ki sayar da kuri’arta saboda tana muradin makoma mai kyau. Ta shawarci masu kada kuri’a su guje wa sayar da kuri’unsu.

“Sayar da kuri’u ba ya da kyau. Tamkar muna sayar da makomarmu ce, sai mun dandana dacinsa nan gaba; ta yaya za ka yi tsammanin mutumin da ya kashe makudan kudi wajen sayen kuri’arka zai fanshi kudadensa. Ba daidai ba ne,” inji ta.

Wani mai shekara 69, Injiniya Adebayo Abdulfatai, ya ce ya fara kada kuri’a tun 1979, ya ce yayin sayen kuri’un shi ma nan ba da dadewa ba zai kau ya zama tsohon yayi saboda yadda masu kada kuri’ar ke kara wayewa sannan hukumar zabe take inganta tsarin zabubbuka a kullum.

“Ina kira ga mutane su daina sayar da kuri’a in suka ki, to lokaci zai kawar da abin. Ka duba lokacin muna kanana, kuri’ar mutum ba za ta yi tasiri ba saboda suna sace akwatin zaben, su rubuta sakamakon da suke so amma wadannan ababuwa yanzu sun kau.

Haka shi ma batun sayen kuri’un zai kau nan gaba, in mutum ya kashe makudan kudi sannan ya sha kaye. A nan zai gane ba kudi ne zabe ba.

Halinka jarinka ne kawai, ba nawa ka raba wa mutane ba. Za mu kai matakin da kokarinka ne kadai zai fisshe ka a wurin masu kada kuri’a ba kudinka ba,’’ inji shi

Yadda za a hana sayar da kuri’a

Masana sun ce Hukumar INEC tana iya kassara sayar da kuri’a ta hanyar tabbatar da an bi ka’idojin sirrinta dangwala kuri’a kamar yadda doka ta tanada.

Sun ce da taimakon jami’an tsaro, Hukumar INEC za ta iya hana kamfe da zawarcin kuri’un jama’a a kusa da rumfunan zabe.

A cewarsu, sirrinta dangwala kuri’a na samun tasgaro ne lura da cewa ma’aikatan INEC dinda kansu suke ajiye tantin kada kuri’ar a wajen da wakilan jam’iyyu suke iya hangen wanda mai kada kuri’a ya zaba.

Kungiyar YIAGA Africa ta roki INEC ta tabbatar da sirrinta kada kuri’a a kullum.

“Ya kamata INEC ta ci gaba da dabbaka tsarin sirrinta kuri’a ta hanyar tabbatar da tantunan kada kuri’a da akwatunan zabe an ajiye su wajen da zai sirranta kuri’ar mutum,” kamar yadda ta fada a rahotonta.

Ta ba da shawara ga jami’an tsaro su tabbatar sun hukunta duk wani nau’i na yi wa Dokar Zabe karan-tsaye a ranar zabe, musamman duk wata barazana ga jefa kuri’a ko yunkurin sayen kuri’a.

Ita kuwa Gidauniyar CLEEN, a nata rahoton, ta yi kira a dauki mataki a kan sayen kuri’a da sauran laifuffukan zabe, domin katse hanzarinsu daga zama ‘sababbin dabarun magudin zabe’, musamman a zaben 2023 da ke tafe.

Wani mai sa-ido a zabe kuma Babban Sakatare a Gamayyar Kungiyoyin Dimokuradiyya a kan Zaben 12 ga Yuni (J12CODEF), Nelson Ekujumi, ya ce akwai bukatar a kara ilimantarwa tare da wayar da kan jama’a kan illar sayar da kuri’a.

“Abin takaici, a lokacin zabe, masu jefa kuri’a su dauki lokacin tamkar lokaci ne na sharbar jar miya a gidajensu.

“Muna bukatar kara ilimantarwa da wayar da kan jama’a ta hanyar ci gaba da sanar da su dalilin da ya sa bai dace su sayar da kuri’unsu ba,” inji shi.

An kuma bukaci Hukumar EFCC ita ma ta gurfanar da wadanda aka kama suna sayen kuri’un da wadanda suka dauki nauyinsu.