✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda siyasar munafunci take hallaka al’umma (1)

Daga hudubar Sheikh Waddah bin Yusuf Al-Jabaziyyu Masallacin Al’urwatul Wuska Fassarar Salihu Makera   Godiya ga Allah da taslimi ga Annabi (SAW). Bayan haka, lallai…

Daga hudubar Sheikh Waddah bin Yusuf Al-Jabaziyyu

Masallacin Al’urwatul Wuska

Fassarar Salihu Makera

 

Godiya ga Allah da taslimi ga Annabi (SAW).

Bayan haka, lallai mafi hadarin cutar da take barazana ga al’umma, kuma take rusa karfinta, kuma take yi mata kaca-kaca, ita ce munafunci. Munafunci yana haifar da tufka da warwara ga halin mutum, sai mutum ya rika bayyana sabanin abin da ke boye a zuciyarsa, ya rika fadin abin da ba zai aikata ba, ya yi alkawari ya saba, kuma ya yi yaudara, sannan yayin husuma, sai ya yi fajirci.

Mafi munin illarsa kuma wanda ya fi watsuwa a yau, shi ne idan munafunci ya zamo siyasa abar bi, ko hanyar da kowa ke sha’awar hawa kanta, musamman a tsakanin shugabannin siyasa a kasashen Musulmi. Halin da muke ciki a yau yana fassara hakan daki-daki, kuma abin bakin ciki wadansu suna alfahari da haka, suna ganin hakan wani burgewa ne.

Saboda hadarin haka Allah Ya fallasa halayen irin wadannan mutane a surori da dama, domin Ya tsarkake al’umma daga sharrin wannan muguwar dabi’a. Sannan kuma Annabi (SAW) mai girma wanda ba ya fadin magana ta son zuciya ya fayyace mana siffofin wadannan mutane cikin fadinsa: “Alamun munafuki uku ne: idan ya yi magana ya yi karya, idan ya yi alkawari ya saba, idan aka ba shi amana ya yi ha’inci, koda ya yi azumi ya yi Sallah, kuma ya zaci shi Musulmi ne.” A wata ruwayar kuma ya ce, “Idan ya yi rantsuwa ya yi yaudara, idan ya yi husuma ya yi fajirci.” Kuma ya ce, “Halaye hudu duk wanda ya tara su, ya zama cikakken munafuki. Wanda kuma yake da yanki daga cikinsu, yana da wani yanki na munafunci har sai ya yi watsi da shi: Wato idan ya yi magana ya yi karya, idan ya yi rantsuwa ya yi yaudara, idan ya yi alkawari ya saba, idan kuma ya yi husuma ya yi fajirci.”

Hakika akwai bukatar mu kange mutanenmu daga masu wadannan halaye, domin kada su kasance bala’i ga daidaikun mutane da daukacin al’umma kamar yadda gara take cin itace, ko yadda sari ke lalata katako idan aka gafala daga gare su, tilas ne mu kasance a fadake kuma a hankalce game da su.

Mu tsaya mu dubi manyan alamomin wadannan mutane makiya gaskiya da suke kare karya. Hakika Manzon Allah  (SAW) ya bayyana ce siffarsu ta farko ita ce: “Idan zai yi magana ya yi karya.” Ibn Taimiyya (Allah Ya yi masa rahama) ya ce:  “Idan aka ambaci munafunci a cikin Alkur’ani, sai a ambace shi tare da karya, kuma idan aka ambaci karya, sai a ambace ta tare da munafunci. Allah Madaukaki Ya ce: “Suna yaudarar Allah da wadanda  suka yi imani, alhali ba su yaudarar kowa face kawunansu, amma ba su sani ba. A cikin zukatansu akwai cuta, sai Allah Ya kara musu wata cutar, kuma suna da azaba mai radadi saboda abin da suka kasance suna karyatawa.” (K:2: 8-9). A cikin Suratu Tauba Allah Ya ce: “Kuma Allah Ya shaida, su (munafukai) wallahi makaryata ne.” A nan Allah Ya ambaci karya. Kuma idan Allah Ya ambaci munafunci sai Ya ambaci karancin zikiri, (ambato ko tuna Allah). Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma (su munafukai) ba sa ambato ko tuna Allah face kadan.” Sannan a wata ayar cikin Suratu Munafikun Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Kada dukiyarku da ’ya’yanku su kange ku daga ambaton Allah…”

Allah Ya kore munafunci daga muminai, saboda zikiri ko tuna Allah da suke yi, sannan Ya siffanta munafuncin munafukai da karancin zikiri ko tuna Allah.

Masu karya la’anannu ne, don haka mutane su guji wannan dabi’a abar zargi. Lallai ginshikin munafunci kuma babban rukuninsa da kusoshin da suke rike da shi da turakun da suke tokare shi da da’irorin da suka kewaye shi, ita ce karya. Munafukai ba za su yi munafunci ba face sai sun yi karya a cikin zukatansu. Munafunci yakan fara ne da wani digo a cikin zuciya, ya rika girma har sai ya zama babbar shimfida kuma ganuwa mai hana imani wurin zama, Allah Ya tsare mu. Wannan ne ya sa ake cewa, “Wanda ya ginu a kan karya sai abincinsa ya yi zaki,” ma’ana duk wanda rayuwarsa ta saba da karya zai yi wuya ya daina ta, maimakon haka zai ci gaba da karyar ce iya tsawon rayuwarsa.

Wani ya ce: “Mutum ba ya yin karya face wulakantacce ko mai mugun aiki ko mai karancin ladabi.”

Alama ta biyu: Yaudara da ha’inci. Dalili fadinsa (SAW): “Idan ya yi alkawari ya yi yaudara.”

Duk wanda ya yi alkawari ga wani mutum ko mutane ko kungiya, sannan ya yi ha’inci ko yaudara, to wannan alama ce kuma rukuni ne daga cikin rukunan munafunci. Allah Madaukaki Ya ce: “Suna yaudarar Allah da wadanda suka yi imani, alhali ba su yaudarar kowa face kawunansu, amma ba su sani ba.” (K:2:8).

Na uku, fajirci yayin husuma: Saboda fadinsa (SAW) a cikin Sahihaini, “Idan ya yi husuma ya yi fajirci.” Wani malami ya ce: “Wanda ya yi husuma da Musulmi, sannan ya yi fajirci a husumarsa, hakika Allah Ya shaida cewa abin da ke cikin zuciyarsa shi fajiri ne munafuki.” “Daga cikin mutane akwai wanda maganarsa take burge ka a rayuwar duniya, alhali Allah Ya shaida abin da ke cikin zuciyarsa shi mai tsananin husuma ne.” Kuma (SAW) ya ce:  “Mafi muni maza a wurin Allah shi ne mai tsananin yawan husuma.”

Za ka ga fajiri yana cin zarafin mutane ta hanyar husuma, ba ya jin kunyar amfani da miyagun kalamai da tsanantawa domin ya musguna wa wanda ya saba masa.

Bai damuwa ya jawo tashin hankali ko wahala ko cuta ko rauni ko kisa, kansa kawai ya sani, wannan yana daya daga cikin siffofin munafukai.

Daga cikin siffofinsu har wa yau akwai wulakantawa da yada barna. Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai idan munafukai da wadanda suke da cuta a zukatansu da masu rarraba kan mutane a cikin Madina ba su hanu ba, za Mu shushuta ka (dora ka) a kansu, kuma ba za su makwabce ka ba a cikinta face kadan.”

Munafukai suna sabbaba rarrabuwar kan mutane da yada karairayi a tsakanin mutane domin firgitar da su ta yadda za su haifar da gaba da kiyayya a tsakaninsu.

“Suna nemanku da fitina, kuma a cikinku akwai ’yan leken asirinsu, kuma Allah Masani ne ga azzalumai.”

Sai kuma watsa fasadi a cikin kasa da sunan gyara. “Kuma idan aka ce musu; “Kada ku yi barna a cikin kasa,” sai su ce, “iyaka mu masu gyara ne.” A’a (karya suke yi) su masu fasadi ne, amma ba su sani ba.”

Munafukai suna aikata abin da zai tayar da fitina kamar wutar daji su kona gidaje, su ruguza zamantakewar jama’a, su daidaita al’umma. Idan aka ce musu, kuna bata al’amura tare da rarraba kan jama’a, sai su ce: “Wallahi ba mu nufin komai face gyara,” alhali sun san barna da fasadi suke nufi. Mafi yawan masu bata tsakanin iyali da al’umma da kabilu da zamantakewar jama’a su ne wadannan munafukai. Allah Ya ce: “Daga cikin mutane akwai wanda maganarsa take burge ka a rayuwar duniya, amma Allah Yana shaida a kan abin da yake cikin zuciyarsa shi mai tsananin husuma ne. Idan ya juya a cikin kasa sai ya rika fasadi a cikinta ya hallaka abinci da zuriya, kuma Allah ba Ya son fasadi.”

Suna tsoron aukowar tsawa: “Suna zaton kowace tsawa a kansu take.” Kuma su a kullum suna cikin tsoro, suna cikin firgici, suna tsorace, suna kuma cikin kai-kawo a rayuwarsu.

Suna umarni da abin ki suna hana aikin alheri: Kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce: “Munaukai maza da munaukai mata, sashinsu majibintan sashi ne; suna umarni da abin ki, suna hana aikin alheri, kuma suna damke hannunwansu (rowa). Sun mance da Allah, sai Ya mance da su, lallai munafukai su ne fasikai.”