✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sojoji suka ragargaji ISWAP da Boko Haram A Borno

Dakarun Najeriya na Operation Hadin Kai sun dakile hare-hare uku na kungiyoyin ISWAP da Boko Haram a Arewa maso Gabashin Jihar Borno

Dakarun Najeriya na Operation Hadin Kai sun dakile hare-hare uku na kungiyoyin ISWAP da Boko Haram a Arewa maso Gabashin Jihar Borno, inda suka kashe da dama daga cikin ’yan ta’addan.

Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa an kai hare-haren ne a ranar 4 ga Afrilu, 2023, a Njimtilo da Pulka da Ajiri Mafa, amma sojojin suka yi gaggawar murkushe su.

Majiyar ta ce ’yan ta’addar sun yi yunkurin kai hari kan sojojin bataliya ta 73 da aka girke a cibiyar koyar da sana’o’i (Morroco) a Njimtilo, kusa da Maiduguri, amma sojojin suka fatattaki ’yan ta’addan da suka tsere da raunukan harbi.

A wata arangamar kuma, mayakan Boko Haram da ba a tabbatar da adadinsu ba, wadanda ake zargin sun fito ne daga sansanin Ali Ngulde da ke Tsaunin Mandara sun yi yunkurin kutsawa cikin garin Pulka, amma jami’an tsaron hadin guiwa da aka girke a Makarantar Firamare ta Damra, suka kashe biyar daga cikinsu, yayin da wasu suka gudu.

A ranar Alhamis kuma, mayakan ISWAP da dama sun kai hari a wani sansajin sojoji a Ajiri Mafa, amma nan take aka fatattake su tare da kashe wasu da kuma ji wa wasu da dama raunuka.