✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sojoji suka yi raga-raga da ’yan ta’adda a Dajin Sambisa

Jiragen yakin sojojin Najeriya biyu na Super Tucano sun yi raga-raga da mayakan Boko Haram da ISWAP masu yawan gaske a maboyar ’yan ta'addan a…

Jiragen yakin sojojin Najeriya sun yi raga-raga da ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP masu yawan gaske a maboyarsu a Dajin Sambisa.

Jiragen yakin sun yi raga-raga da ’yan ta’addan ne bayan sun ritsa su a wani wuri da ake kira Somaliya, inda ake kyautata zaton a nan ’yan ta’addan ke jinyar mayakansu da suka samu raunuka.

Rahoto ya nuna baya ga kashe mayakan ISWAP a wurin, jiragen yaki sun kai hari a yankin Abdallari, wani maboyar ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabashin Maiduguri.

Majiyar Aminiya ta shaida mata cewa, an hallaka ’yan ta’adda da dama tare da lalata gidadjensu su da bama-bamai.

Majiyar ta kara da cewa a jihohin Neja da Kaduna, rundunar sojin sama ta Operation Whirl Punch ta kai makamancin wannan farmaki kan maboyar ’yan bindigar daji.

Ya ce: “An kai harin ne a Kaduna a ranar 7 ga Satumba 2022 bayan wasu bayanan sirri da aka samu daga maboyar ’yan ta’adda a Gidan Waya, Karamar Hukumar Chikun.

“Rundunar Operation Whirl Punch ta wasu gine-ginen ’yan ta’addan da suka boye a karkashin bishiyoyi a wurin tare da ganin ayyukan ’yan ta’addan a yankin.

Da aka tuntubi kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da kai haren -hare na ISWAP da ’yan bindiga.

Gabwet ya ce: “Dakarunmu na ci gaba da mamaye sassan kasar da ke fama da rikici tare da hadin gwiwar sojojin kasa don kawar da ’yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya a Najeriya,” in ji shi.