✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda UEFA ta fitar da jadawalin Gasar Zakarun Turai ta bana

Rabon Newcastle United da haskawa a Gasar Zakarun Turai tun kakar wasa ta 2002/2003.

Hukumar UEFA ta fitar da sabon jadawalin Gasar Kofin Zakarun Turai na bana, wanda ke kunshe da kungiyoyi 32 wadanda aka karkasa zuwa rukunnai 8 wato kungiyoyi 4 a duk rukuni guda.

Jadawalin na UEFA ya nuna cewa Newcastle United wadda sabuwa ce a gasar za ta hadu da manyan kungiyoyin Turai irin su PSG da Bayern Munich da kuma AC Milan, wadanda dukkaninsu suka iya nasarar kai wa wasan karshe na gasar cikin shekaru 16 da suka gabata.

Rabon Newcastle United da haskawa a gasar ta Kofin Zakarun Turai tun kakar wasa ta 2002 zuwa 2003 wanda ke nuna kakar ta bana za ta zo mata da gagarumin kalubale duk da rawar ganin da ta taka a kakar da ta gabata karkashin gasar Firimiya har ta kai ga kammalawa a sahun ‘yan hudun saman teburi, da ya bata damar samun tikitin gasar ta zakarun Turai.

Ga yadda jadawalin na UEFA ya ke aka fitar a ranar Alhamis:

A rukunun A na farko ke nan akwai kungiyoyin Bayern Munich da Manchester United da FC Copenhagen baya ga Galatasaray.

Rukunin B na kunshe da Sevilla da Arsenal da PSV Eindhoven baya ga RC Lens.

Rukunin C kuwa akwai Napoli da Real Madrid da Braga baya ga Union Berlin.

Rukunin D akwai Benfica da Inter Milan da Salzburg baya ga Real Sociedad.

Rukunin F na kunshe da PSG da Borussia Dortmund baya ga AC Milan da Newcastle United.

Rukunin G akwai Manchester City mai rike da kanbu kana RB Leipzig da kuma Red Star Belgrade kana Young Boys.

Rukunin H kuma na karshe na kunshe da kungiyoyin kwallon kafa na Barcelona da Porto da Shaktar Donetsk da kuma Royal Antwerp.

Dukkanin wasannin rukuni za su gudana ne tsakanin ranar 19 ga watan Satumba zuwa 13 ga watan Disamba, gabanin a tsallaka rukunai daban-daban na gasar a kuma doka wasan karshe a ranar 1 ga watan Yuni da zai gudana a filin wasa na Wembley da ke Landan.