✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Umar Fadar Bege ya rasu

Cikin makon da ya wuce ne Allah Ya yi wa shahararren mawakin yabon Manzon Allah (SAW), Umar Abdul Azeez wanda aka fi sani da Fadar…

Cikin makon da ya wuce ne Allah Ya yi wa shahararren mawakin yabon Manzon Allah (SAW), Umar Abdul Azeez wanda aka fi sani da Fadar Bege, rasuwa.
Aminin marigayin Malam Hafizu kuma daya daga cikin wadanda suka yi jinyar marigayin  da shi , ya ce: “Ba kamar yadda mutane suke rade-radi ba, Umar ya rasu ne a sakamakon rashin lafiya wanda ya yi ta fama da ita, amma ba jifa ba ne ko hadari ko kuma wani dalili da mutane suke ta cece-kuce ba. Matsalar daukewar numfashi ne a sakamakon wani abu kamar majina da take damunsa a kirji.”
“Umar ya soma wannan rashin lafiya ne a tsai-tsaye tun ashirin da uku ga watan azumi, a inda ya same ni a gida ya ce min in kai shi asibiti, na kai shi asibiti, an duba shi an ba shi magani, amma tsawon wannan lokaci bai rabu da wannan larurar b a, sai  dai ya kwanta ya tashi; yau da lafiya gobe babu lafiya. Amma duk da haka mun yi majalisi da shi a Gombe da Nasarawa da sauransu wasu garuruwa.
Cutar dai ba ta ci karfinsa ba sai gabannin Babbar Sallah a inda ya kira aminin nasa a waya amma ya kasa magana da shi, sai matarsa Ramla ta ce asibiti za a kai shi jikin ya yi tsanani. Daga nan ya kai shi asibitin kudi  a Sharada a inda ganin yadda numfashinsa yake daukewa, suka sanya masa na’urar yin numfashi ta Odygen. Bayan wani lokaci sai asibitin suka ce musu odygen din su za ta kare cikin minti talatin sai dai su je asibitin gwammanti. Suka rubuta musu takarda, daga nan sai  asibitin Aminu Kano. A nan ana yajin aiki. Sai suka tafi Asibitin Nasarawa, a nan babu gado, A asibitin Murtala kuma nasu ya kare. Sai suka tafi Asibitin Zana watau IDH. Nan kuma ba su da Odygen. A takaice ce sai da suka je asibitoci biyar sai daga karshe a wani asibiti mai zaman kansa ya karbe su, aka kuma sa masa abin numfashi na Odygen. Cikin wannan hali Umar ya galabaita domin tun misalin Azahar suke yawo har sai da suka kai bayan isha.
Ya ce: “A wannan  asibiti aka yi shawarar  yi masa aiki ta makoshinsa domin fidda numfashi watau ‘bypass’. Sai dai matsalar a nan ita ce zai rasa muryarsa kuma idan aka huda zai yi kamar shekara biyar kafin ya warke. Ba a yi aikin ba amma an sa masa odygen kuma numfashinsa ya dawo. A nan ma yake ce mini shi fa mutuwa zai yi, na ce masa, a’a. Kuma Allah Ya sa har ya samu sauki, domin a wannan hali na ba shi takarda ya soma rubuta kasida wacce na ba shi amshinta. Da hannunsa ya rubuta Bismilla. Ya kuma cire abin numfashinsa.
“Bayan mun koma gida sai jikin ya rikice, ma’ana numfashinsa ya rika daukewa sai ya rika salati yana hailala a tsakani. kafafuwansa su ka yi sanyi, sai muka garzaya da shi asibitin Nasarawa ashe shirun da muka ji ashe ya cika. Muna isa wani likita wanda ya san shi, ya tabbatar mana da hakan.” Inji shi.
Umar Abdul Azeez wanda aka fi sani da Fadar Bege, mutumin Wudil ne ta Jihar Kano, kuma almajirin Sidi Shariff Sani na Jan Bulo ne. Malam Umar  ya wallafa wakokin yabon Manzon Allah (SAW) masu yawa. Cikin wakokin da suka yi fice akwai ‘Labbaika Rasulullah’ da ‘Ahlan Wasahalan ya shugabana’ da sauransu.