✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

WhatsApp ya sake daukewa tsawon mintuna ba ya aiki

Wannan dai ba shi ne karon farko da WhatsApp ya daina aiki ba.

Manhajar sadarwa ta sada zumunta ta WhatsApp ta sake samun matsala inda ta tsaya da aiki na tsawon mintuna a ranar Laraba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da manhajar ta sada zumunta ta samu matsala ba.

A shekarar da ta gabata manhajar ta samu matsala a kasashe da dama ciki har da nahiyar Turai.

Lamarin da ya sanya miliyoyin mutane samun tsaikon tura sako ko karbar sako.

Kamfanin WhatsApp ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana cewar yana aiki tukuru don daidaita komai game sa manhajar.

Sai dai bayan shafe tsawon kusan minti 20 zuwa sama manhajar ta dawo aiki.

A wannan karo ma bincike ya gano cewar daina aiki manhajar ya shafi kasashe da dama na duniya da ke amfani da kafar sada zumuntar.