✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan daban daji 30 suka fada tarko a Katsina

Akalla ’yan daban daji 30 mazauna gari suka kashe a wani kauye da ke Jihar Katsina.

Akalla ’yan daban daji 30 mazauna gari suka kashe a kauyen Majifa da ke Karamar Hukumar Kankara a Jihar Katsina.

Mazauna kauyen gami da ’yan sa kai ne suka yi wa ’yan daban dajin kofar rago, lamarin da ya kai ga sun murkushe su farat daya kamar yadda wani mazaunin kauyen ya shaida wa wakilnmu.

“Bayan da muka samu labarin cewa ’yan daban dajin na shirye-shiryen kawo mana hari cikin dare, sai muka yi musu kwanta-kwanta kuma cikin taimakon Allah muka dakile hari har muka kashe 30 daga cikinsu.

“A yayin da muka jira zuwa wayewar gari don mu kone gawarwakin, ashe tuni sauran ’yan uwansu sun biyo dare sun kwashe gawarwakin a kan rakuma,” in ji shi.

Wannan shi ne karo na uku cikin makonni uku da mazauna ke tunkarar ’yan bindiga a Jihar Katsina.

A Lahadin da ta gabata ce mazauna kauyen Magama da ke Karamar Hukumar Jibia a Jihar suka fafata da maharan kuma suka samu nasarar kashe uku daga cikinsu.

Hakazalika, mazauna kauyukan ‘Yan Marafa da Mununu da ke Karamar Hukumar Faskari ta Jihar, sun yi fito-na-fito da ’yan bindiga, kuma suka yi galaba a kansu.

A wani rahoto mai nasaba da wannan Aminiya ta ruwaito, ’yan bindiga sun kashe wani tsohon Darakta a Ma’aikatar Ilimi ta Karamar Hukumar Danmusa da ke jihar Katsina.

Wannan lamari ya faru ne da misalin karfe 7.30 na Yammacin ranar Laraba yayin da ’yan bindigar suka far wa mutumin a kofar gidansa da ke Danmusa.

“A kan hanyar asibiti ajali ya katse masa hanzari, bayan maharan sun yi kokarin tafiya da shi amma ya tirje, sai kawai suka harbe shi suka tsere,” a cewar wata majiya.

Neman jin ta bakin Kakakin rundunar ’yan sandan Katsina, SP Isah Gambo ya ci tura a yayin da ba iya samunsa ba yayin tattara wannan rahoto.