✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a yi buda baki a masallacin Annabi a watan Azumin bana

Za a kididdige yawan jama’ar da ake bukata wajen buda bakin.

A ci gaba da shirye-shiryen tunkarar watan Azumi na shekarar 1443 bayan Hijira, hukumomin da ke kula da masallacin Annabi Muhammad SAW a birnin Madina, sun  fitar da tsare-tsaren buda baki na bana.

Tsare-tsaren sun hadar da ka’idodin yadda masu bayar da sadakar abinci da masu buda baki kamar yadda hukumar gudanarwar masallacin ta bayyana.

Ga dai ka’idodin da mahukuntan suka fitar kamar haka:

  • Za a bar wadanda suke da lasisin kawo abincin shan ruwa su ci gaba kamar yadda suka saba a baya.
  • Za a kididdige yawan jama’ar da ake bukata wajen buda bakin.
  • Masu rabon abinci za su tuntubi kamfanonin da aka yarjewa dafa abinci domin su shirya masu abincin da za su bayar.
  • Mutum biyar ne kawai za su zauna a kan kowace shimfida idan akwai bukatar ba da tazara yayin gudanar da buda bakin.
  • Mutum 12 kacal aka bai wa damar zama idan ba a bukatar bayar da tazara yayin buda bakin.
  • Dole a zauna bangaren da za a fuskanci alkibla kadai.
  • Sabunta bayanai zai fara ne daga watan Rajab.