✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ku kare lafiyar kunnuwanku

Matakan da za ku bi domin kare lafiyar kunnuwanku.

Kare lafiyar kunnenku yana da muhimmanci. Bin waɗannan matakan na iya taimakawa wajen sanya ku a kan hanya  don samun lafiyar kunnuwa da kuma kula da jinku.

Kada ku jira har sai lokaci ya kure kafin  ku fara damuwa da lafiyar kunnenku.

*Kula da ƙarar na’urorinku. Ku rage ƙarar TV, rediyo, kiɗa, da sauransu, yayin da kuke kallon TV ko sauraren rediyo.

Bai kamata ba karar ta yi  ƙarfi sosai har a rika jin ta daga wani ɓangaren gidanku.

*In kuna jin sautuka masu ƙarfi kamar kade-kade, ku rika kashewa kuna hutawa daga hayaniyar.

Rage sauraren kiɗa a wayoyinku tare da ƙara karfin sautin ya haura kashi 60 cikin dari har tsawon sama da sa’a ɗaya.

Wannan zai  kare kunnuwa daga lalacewa, kuma ya kamata a ce ba kullum ake jin sauti ba.

*A guji zuwa wurare masu hayaniya. Kunnuwanmu  kamar sauran jikinmu suna buƙatar lokaci don hutawa da murmurewa.

Idan kullum ana wajen da yake da kara sosai, ya kamata a rika hutu kowanne minti kaɗan.

*Kada ku sanya wani abu a kunnenku. Wannan ya haɗa da auduga, allura, kusa, mabudi, tsinke, ko wani abu da za ku iya amfani da shi don kuje kunnenku.

*A dinga zuwa wajen likita don duba kunne ko idan kun ji sauyi a kunnenku, ko wata irin kara ko nauyi a cikin kunnuwanku sama da awanni 24.

Rashin ji yana samuwa saboda dalilai da yawa, amma waɗannan dalilan ana iya kauce musu.

Daukar lokaci mai tsawo ana sauraron ƙara mai ƙarfi na iya lalata jijiyoyi a cikin kunnenmu.

Ta hanyar kare kunnuwanku, kuna iya tsira daga lalacewar jijiyoyin.