✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yajin Aiki: Na kori duk Ma’aikatan Jinya ’yan kasa da matakin aiki na 14 — El-Rufai

Har kawo yanzu Kungiyar Kwadagon ba ta yi martani a kan lamarin ba.

Gwamna Malam Nasir El Rufai ya kori dukkanin ma’aikatan jinya na Jihar Kaduna wadanda ba su haura matakin aiki na 14 ba.

Matakin da Gwamnan ya dauka na da nasabda ne da wani sako da Gwamnatin Jihar ta wallafa a shafin Twitter, inda ta yi zargin cewa a ranar Litinin ma’aikatan jinyar sun cire bututun iskar oxygen da ke taimaka wa wani jariri dan kwanaki biyu da haihuwa shakar numfashi a Asibitin Koyarwa na Barau Dikko yayin da suka shiga yajin aikin Kungiyar Kwadago.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da dukkanin al’amuran tattalin arziki suka tsaya cik yayin da Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC ta tsunduma yajin aikin kwana biyar domin gargadin Gwamnatin Jihar ta janye sallamar dubban ma’aikata da ta yi.

Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan a Kafafen ssadarwa, Muyiwa Adekeye ya fitar, ta ce, “baya ga neman Ma’aikatar Shari’a ta hukunta Ma’aikatan jinyar, gwamnati tana kuma sanar da korar su dukkanin ma’aikatan jinya ba su haura matakin aiki na 14 ba saboda yakin aikin da suka shiga ba bisa ka’ida ba.

“An bai wa Ma’aikatar Lafiya umarnin ta tallata neman sabbin ma’aikatan jinya cikin gaggawa domin maye gurbin wadanda aka kora sannan albashinsu za a bai wa ma’aikatan da suka ci gaba da aikin a matsayin lada.

“Gwamnatin tana kuma umartar dukkanin ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomi a Jihar da su gabatar da rajistar ma’aikatan da ke zuwa aiki ga Shugaban Ma’aikatan Jihar, yayin da kuma ake umartar Jami’ar Jihar Kaduna ta gabatar da rajistar ma’aikatanta masu zuwa aiki ga Sakataren Gwamnati Jihar da kuma Kwamishinan Ilimi” a cewar sanarwar.

Sai dai har kawo yanzu Kungiyar Kwadagon ba ta yi martani a kan lamarin ba.