✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aikin ma’aikatan jami’a ya gurgunta al’amura a Jami’ar Bayero

Idan kwanakin suka cika ba tare da an dauki mataki ba, za mu tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

Yajin aikin da Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU) ta shiga ya gurgunta al’amura da dama a Jami’ar Bayero da ke Kano.

A zagayen da Aminiya ta yi a Jami’ar, ta gano cewa dakunan karatu da dama suna garkame yayin da ’yan kadan din da suka rage aka bar su babu shara.

Hakazalika, azuzuwa da sauran dakunan karatun jami’ar sun kasance a garkame da kwado.

Aminiya ta rawaito cewa, Kungiyar ta SSANU ta shiga yajin aikin na gargadi a yau Litinin don nuna damuwarsu game da yadda Gwamnatin Tarayya ta yi shagulatan bangaro da bukatunsu.

Mustapha Aminu, Shugaban SSANU reshen Jami’ar Bayero ya bayyana cewa za su shafe tsawon mako guda suna gudanar da yajin aikin

Da yake bayani game da bukatun na ’ya’yan kungiyar, Mustapha Aminu ya ce Gwamnatin Tarayya ta gaza cika yarjejeniya da suka kulla da ita tun a shekarar 2009 ciki har da karin kaso 25/35 na albashinsu da kuma biyan bashi na karin albashin bai daya da aka yi.

Haka kuma, kungiyar ta ce tana bin Gwamnatin Tarayya bashin Naira Biliyan 50 da ta yi alkawarin ba su na alawus-akawus dinsu.

Shugaban na SSANU ya kuma yi gargadin cewa babu wani mambansu da zai yi wani aikin taimako a ofisoshinsu daban-daban.

Haka kuma, a cewarsa idan har kwanaki bakwai sun cika kuma gwamnatin ba ta yi abin da ya kamata ba, to za su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.