✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yake-yake: Tibi da Fulani sun sasanta a Taraba

Fulani da Tibi sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu a Jihar Taraba.

Shugabanin kabilun Tibi da Fulani sun amince su dakatar da kashe-kashe da ke aukuwa a tsakanin bangarorin a Jihar Taraba.

An yi sulhun ne bayan taron da shugabanin Tibi da Fulani suka gudanar a garin Jalingo a ranar Lahadi inda suka kulla yarjejeniyar ajiye makamai su zauna lafiya a tsakaninsu.

Yarjejeniyar zaman lafiyar, wadda Sarkin Fulanin Bali, Alhaji Adamu Abacha da Shugaban Tibi na Bali, Mista David Zaki Gbaa suka sanya wa hannu ta amince da cewa duk wadanda yakin ya raba da garuruwansu su koma gidajensu.

An kuma amince a kafa kwamiti mai mutane 15 daga kabilun biyu domin wayar da kan jama’arsu kan muhimancin zaman lafiya.

Sun kuma amince cewa bangarorin za su sa ido domin hana masu hura wutar fitina a tsakanin Tibi da Fulani su sake haddasa wata rigima a tsakaninsu a nan gaba.