✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga 7 sun mika wuya a Zamfara

'Yan bindigar sun yi tuba tare rantsuwa da Alkur'ani a gaban Gwamnan Jihar.

’Yan bindiga daga jihohin Kaduna da Neja da kuma Yobe sun mika wuya a jihar Zamfara tare da mika makamansu.

Daga cikin makaman da tubabbun ’yan bindigar suka mika akwai bindigu kirar AK47 guda 14, wasu bindigun guda 47 sai harsasai da dama, sannan suka rantse da Alkur’ani cewar sun tuba.

‘Yan bindigar guda bakwai sun mika wuyan ne a gaban Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle da Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Mista Abutu Yaro da Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello.

“Jami’an tsaro za su ci gaba da bankado maboyar ‘yan bindiga, matukar ba za su tuba su mika wuya ba, kuma za su fuskanci fushin hukuma,” inji Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar.

Mallam Abubakar Fari, yayin da yake musu nasiha

Ya kuma ce ya zuwa yanzu, jihar ta samu nasarar kwato bindigu 107 da wasu makamai daga hannun ‘yan bindigar da suka mika wuya tun shekarar 2019.

A cewarsa, kowanne daga cikin ‘yan bindigar da suka mika wuyan, na dauke da Alkur’ani yayin da suke rantsuwar.

Shugaban limaman jihar ta Zamfara, Mallam Abubakar Fari shi ne ya jagoranci karbar rantsuwar ta su.

Yayin da yake jawabi, Gwamnan Matawalle ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar ya shaida masa cewar karin wasu ‘yan bindigar ma na da niyyar tuba tare da mika wuya ga Gwamnatin Jihar.

Ya kara da cewa hanyar tattaunawa da ‘yan bindigar cikin masalaha na haifar da kyakkyawan sakamako.

Daga nan sai ya ja kunnen ragowar ‘yan bindigar da suka addabi jihar, da su tuba su mika wuya ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Ya ce jami’an tsaro suna ci gaba da fito da sabbin dabaru wajen bankado maboyar bata-garin kuma za su ga bayansu nan ba da jimawa ba.