✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga na shirye-shiryen kawo min hari — Dikko Radda

Ana jigilar kayan abinci daga kasuwanninmu zuwa kasashe makwabta kamar Nijar, har zuwa Mali da Burkina Faso.

Gwamnan Katsina Umar Dikko Radda ya bayyana cewar ’yan bindigar da jami’an tsaro suka hana sakat a jihar na ci gaba da farautarsa domin kawo masa hari, sai dai hakan ba zai sa ya ɗaga kafa a kokarin sa na kakkabe su daga jihar domin tabbatar da zaman lafiya ba.

Gwamnan ya ce bayanan sirri kan harkokin tsaro sun tabbatar da haka, amma ko da sunan wasa babu abin da zai razana shi wajen ganin ya kauda kai daga alkawarin da ya yi wa Katsinawa na samar musu zaman lafiya.

Radda ya bayyana cewar nasarar da ake samu a kan ’yan ta’addan shi ne ke musu zafi, saboda haka jami’an tsaro za su ci gaba da aikin su wajen ganin an samu cikakken zaman lafiya a jihar.

“Rahoton tsaro ya nuna cewa a yanzu ina ɗaya daga cikin waɗanda suke ƙoƙarin kaiwa hari a jihar saboda matakan da muke ɗauka na shawo kan lamarin.”

Gwamna Radda yayin yi wa Sarakunan Katsina gaisuwar ban girma.

Gwamnan ya kuma bayyana matukar damuwa a kan yadda ake safarar abinci daga Najeriya zuwa kasashen makota, abin da ke haifar da tsadar su yanzu haka.

“Abin takaici ne yadda farashin kayayyakin abinci da sauran kayayyakin masarufi ke karuwa a kullum, don haka akwai buƙatar masu ruwa da tsaki su ba da shawarwari masu amfani a kan matsalar.

“An sanar da ni cewa ana jigilar kayan abinci daga kasuwanninmu zuwa kasashe makwabta kamar Nijar, har zuwa Mali da Burkina Faso, saboda darajar Nairar mu ta tabarbare yayin da nasu kuɗaɗen ke kara daraja.

“Irin waɗannan mutane suna amfani da wannan damar wajen cutar da talakawa. Wannan babbar matsala ce da ba za mu iya nade hannayenmu mu kyale ta ci gaba ba.”

Ya bayyana hakan ne yayin gudanar da wani taron gaggawa na majalisar tsaro wanda aka gayyaci sauran jiga jigan jihar domin tattauna wasu daga cikin matsalolin da suka addabe ta, ciki har da da matsalar tsaro da kuma tsadar kayan masarufi.

A taron wanda aka gudanar a ranar Juma’a, Radda ya yi alkawarin kafa kwamitin da zai aiwatar da yarjejeniyar da taron manyan mutanen jihar ya cimma.

Yayin taron wanda ya samu halartar manyan sarakunan jihar, wato Dokta Abdulmumini Jibrin, Sarkin Katsina da Dr Umar Faruk, Sarkin Daura da kuma shugabannin hukumomin tsaro, gwamnan ya ce duk da yake ba a samu irin wannan zanga-zangar a Katsina ba, yana da kyau a ɗauki mataki ganin yadda aka gudanar da ita a wasu jihohi cikin su har da Kano da ke makwabtaka da su.

Fuskokin wadansu daga cikin maharta taron.

Sauran mahalarta taron sun haɗa da Babban Jojin Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar tare da Alƙalin alkalai na jiha, Dokta Muhammad Kabir Abubakar da jami’an gwamnatin da abin ya shafa da malaman addini da ƙungiyoyin ‘yan kasuwa da shugabannin kananan hukumomi da sauransu.