✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘’Yan bindiga sun ci mu tarar N1m saboda kai kudin fansa a makare’

Sun biya karin N1m saboda kai kudin a makare

Wasu miji da mata da ’yan bindiga suka sace a Jihar Katsina sun shaki iskar ’yanci bayan biyan kudin fansa Naira miliyan 11 a maimakon miliyan 10 da suka yi ciniki tun da farko.

Idan za a iya tunawa dai kwanaki 10 da suka gabata ne ’yan bindiga suka kai hari kauyen Shola da ke Karamar Hukumar Katsina a Jihar, inda suka sace mutane shida.

Guda daga wadanda aka sace mai suna Alhaji Tukur ya ce ranar da abin ya faru, shi da mai dakinsa sun jiyo wani na ja in ja da dansu, abin da ya sanya ta bude kofa har ’yan ta’addan suka shiga gidan ke nan.

Mijin ya ce, “Da suka shigo, sun bukaci na ba su kudi, sai na ba su Naira dubu 700 da ke hannuna. Sai guda daga cikinsu ya ce min ba kudina ya kawo su ba, an dakko hayarsu ne su kashe ni.

“Da na tambaye shi a inda zan tsaya su harbe ni sai ya rike hannuna ya ce ba za su kashe ni ba, amma za su tafi da ni saboda na biya kudin fansar kaina.

“Da muka fita, sai matata ta biyo mu, suka yi suka yi da ita ta ki komawa, sai wani a ciki ya ce kawai su tafi da ita, kuma haka aka yi.

“Mun yi tafiya a kafa har kusa da kauyen Bugaje da ke Jibiya, in da ’yan bindigar suka ajiye baburansu, suka kai mu daji”.

“Kashegari sun bukaci na basu Naira miliyan 30, muka yi ta ciniki har muka dawo miliyan 10, to sai dai ruwan sama ya sanya mutane na ba su iya kawo kudin ba.

“Da aka kwana guda sai suka ce sai mun karo miliyan daya saboda bata musu lokaci da muka yi, kuma haka muka biya,” inji mijin.

‘Halin da sauran wadanda aka sace ke ciki’

Turaki ya kwatanta masifar da wadanda aka sace ke ciki a hannun ’yan bindigar, inda ya ce wata mata da suka sato ta haihu, sai dai babu ko kayan sawa na jaririn, hasalima leda ake daura masa don tare najasa, kuma ba maganar yi masa wanka tsawon kwana uku.

A nata bangare matar tasa ta ce ’yan bindiga har da wata mai shayarwa suka sace a unguwar Shola.