✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Bindiga Sun Dauke Mai Shayarwa da Danta a Zariya

’Yan bindiga sun kai tagwayen hare-haren ne a kananan hukomomin Zariya da Sabon Gari da ke Jihar Kaduna. ’Yan sun sace wata mata mai shayarwa…

’Yan bindiga sun kai tagwayen hare-haren ne a kananan hukomomin Zariya da Sabon Gari da ke Jihar Kaduna.

’Yan sun sace wata mata mai shayarwa da danta suka kuma harbi wani matashi a daren ranar Alhamis.

Maharan sun kai faramakin ne a yankin kananan hukumomin Zariya da Sabon Gari a Jihar Kaduna.

A halin yanzu matashin yana kwance a Asibiti Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke domin samun kulawa.

Maharan sun harbi matashin ne a kauyen Tudun Sarki a Kufaina da ke Wusasa Karamar Hukumar Zariya.

Sai dai jami’an tsaro hadin gwiwar sojoji da ’yan sanda da ’yan sa-kai sun samu nasarar kwato maijegon da danta.

Haka kuma maharan sun kutsa Hayin Liman da ke Zangon Shanu, Samaru a karamar hukumar Sabon gari.

Maharan da suka kai farmaki kauyen da misalin karfe daya na daren Juma’a, sun isa yankin ne akan babura dauke da muggan makamai.

Wani ganau da muka zanta da shi da ya nemi a sakaya sunan sa ya ce, “’Yan bindigan sun dauke matar mai shayarwar ne tare jaririnta a kauyen Tudun Sarki; Daga bisani suka wuce kauyen Hayin Liman inda suka sace wani dattijo mai suna Abubakar Garba Aliyu tare da kaninsa, Salimi Abubakar.

“Dattijon ma bai dade da dawowa wannan yankin da zama daga garin samaru ba,” a cewar ganau din.

Zangon Shanu dai wani yanki ne da yawancin mazauna wajen malamai ne da kuma la ma’aikatan Jami’ar Ahmadu Bello da ke Samaru.

Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa ’yan bindigar sun kutso ne ta bayan jami’ar.

Wasu rahotanni na nuni da cewa jami’an tsaro na ci gaba da kokarin kwato dattijon da da suka dauka tare da kaninsa.

Duk kokarin da muka yi na samun kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige ya ci tura, saboda layinshi ba ya shiga a lokacin hada wannan rahoto.