✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun fara dandazo a Kano — Ganduje

Ina neman taimakon rundunar sojin kasa da su kawo mana dauki da gaggawa.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya bayyana fargaba a kan yadda ’yan bindiga suka fara dandazo tare da kafa sansani a wasu dazukan jihar da zummar fara kai hare-hare.

Da yake jawabi ranar Alhamis yayin ziyarar da ya kai Manyan Hafsoshin Soji a Shalkwatar Rundunar Tsaro da ke Abuja, Ganduje ya ce ’yan bindigar sun mayar da dazukan maboyarsu a wani yunkuri na fara kai hari kan al’umma a Jihar Kano.

Gwamnan wanda ya fi bayyana fargaba musamman a kan Dajin Falgore, ya nemi taimakon Rundunar Sojin Kasar da ta tari hanzarin ’yan bindigar gabanin kaddamar da mummunar manufarsu.

“Na kawo muku ziyara ne domin neman taimakon rundunar sojin kasa da su tabbatar da dorewar zaman lafiya a Jihar Kano.

“A yanzu ’yan bindiga sun fara mayar da wasu dazukan Kano maboyarsu, domin sun fara dandazo a Dajin Falgore inda suke shirin kai wa jama’ar mu hari.

“Muna gina makarantu da Asibitoci ga makiyaya a wasu dazukan, amma muna son rundunar sojin kasa ta fara gudanar da ayyukanta a Dajin Falgore.

“Ina rokon Rundunar Sojin Kasa da ta gaggauta kammala ayyukan da take yi samar da sansanin horas da dakarun soji a Dajin Falgore saboda ya zama yana karkashin kulawarta.

Ganduje ya ziyarci dukkanin manyan hafsoshin sojin da suka hada da Hafsan Hafsoshi, Janar Lucky Irabor, Babban Hafsan Sojin Kasa, Manjo-Janar Farouk Yahaya; Babban Hafsan Sojin Sama, Oladayo Amao da kuma Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral A. Z Gambo.

Kazalika, Ganduje ya jajantawa Rundunar Sojin Kasan dangane da rasuwar marigayi Babban Hafsan Sojinta, Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru da sauran dakarun soji da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin jirgin sama makonni biyu da suka gabata.