✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun hallaka mutum 12 a hanyar Sakkwato zuwa Gusau

“Ala tilas, dole matafiya suka rika yin zango har sai da ’yan bindigar suka tafi.”

Wasu mutane da ake zargin ’yan bindiga ne sun hallaka mutum 12 a garin Maikujera da ke Karamar Humunar Rabah ta Jihar Sakkwato.

Da yake tabbatar da kai harin, Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar, ASP Sanusi Abubakar ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Alhamis.

Ya ce akalla mutum 12 ne ’yan bindigar suka hallaka yayin harin.

Sai dai ya ce basu yi garkuwa da kowa ba.

A wani labarin kuma, wasu ’yan bindigar sun tare babbar hanyar Sakkwwato zuwa Gusau ranar Lahadi.

Wani direba, wanda daya ne daga cikin mutanen da lamarin ya shafa a lokacin ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun tare daidai garuruwan Bimasa ne da Lambar Bakura, sannan suka ci gaba da cin karensu ba babbaka na tsawon sa’o’i da dama.

“Ala tilas, dole matafiya da dama suka rika yin zango a garin Bimasa har sai da ’yan bindigar suka tafi,” inji shi.

To sai dai kakakin ’yan sandan na Sakkwato bai tabbatar da faruwar wannan harin ba.