✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbe fiye da manoma 10 a Zamfara

Kwamishinan Tsaro na jihar ya bayyana harin a matsayin mummunan labari.

Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton ’yan fashin daji ne sun harbe fiye da mutum 10 a Jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun far wa mutanen ne a gonakinsu da ke garin Dan Gulbi a Karamar Hukumar Maru.

Shaidu sun ce an kashe sama da mutum 10 tare da jikkata wasu.

Wannan harin na zuwa ne kwana biyu bayan ’yan fashin daji sun yi wa mutum biyar yankan rago a kauyen Kango kamar yadda BBC ya ruwaito.

Kwamishinan Tsaro na jihar Mamman Tsafe ya bayyana harin a matsayin mummunan labari amma yana jiran cikakken bayani.

A bayan nan Gwamnatin Zamfara ta kaddamar da shirin horas da sabbin jami’an tsaron sa-kai da ta dauka domin dakile hare-haren ‘yan bindiga a karkashin kungiyar CPG a takaice.

Bayanai na nuni da cewa an zabo jami’an tsaron na CPG (Community Protection Guards) ne daga dukkanin masarautu 19 da ke fadin jihar.