✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbe wani mutum har lahira

Mahara da ba a san ko su wane ne ba sun harbe wani mai gidan saukar baki na Falola Hotel da ke Ilesa a Jihar…

Mahara da ba a san ko su wane ne ba sun harbe wani mai gidan saukar baki na Falola Hotel da ke Ilesa a Jihar Osun har lahira.

A yammacin Alhamis ne Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Osun, Adie Undie ya tabbatar wa Aminiya aukuwar lamarin a garin Ilesa.

Ya ce rundunar ta fara bincike domin cafko ta kuma gurfanar da ’yan bingidar da suka harbe Mista Falola Oke a kusa da gidansa da ke Ilesa a ranar Laraba da yamma.

Ya ce, “Na bayar da umarnin a gudanar da bincike kan lamarin. Za a mayar da binciken zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Osogbo nan.

“Za a yi cikakken bincike kuma wadanda suka yi danyen aikin za su girbi abin da suka shuka”, inji shi.