✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbe ’yan sa-kai 63 a Kebbi

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun buya ne a kan bishiyoyi, inda suka yi wa ’yan sa-kan kwanton-bauna.

Akalla ’yan sa-kai 63 ne aka tabbatar ’yan bindiga sun harbe a Jihar Kebbi.

Sashen Hausa na BBC ya rawaito cewa lamarin ya faru ne bayan ’yan sa-kan sun kaddamar da farautar ’yan bindigar a masarautar Zuru da ke Jihar.

An dai harbe mutanen ne, wadanda tuni aka riga aka yi musu jana’iza, da sanyin safiyar Litinin.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar dai sun buya ne a kan bishiyoyi, inda suka yi wa ’yan sa-kan kwanton-bauna.

Daga bisani dai sun bude wa ’yan sa-kan wuta bayan da suka riga suka gama yi musu kawanya.

Matasan da aka hallaka din dai sun fito ne daga kauyuka daban-daban na masarautar ta Zuru.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, hukumomin a Jihar ba su ce magantu ba a kan harin.