✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai hari a sansanin soji a Katsina

Sansanin sojin yana Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Shimfida inda aka kashe soja daya da jami'in NSCDS daya nan take suka jikkata wasu

’Yan bindiga sun kashe wani soja da wani jami’in Rundunar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) a wani hari da ’yan bindigar suka kai wani sansanin soji a Jihar Katsina.

Wani ganau ya shaida mana a ranar Alhamis cewa dandazon maharan da suka kai harin da misalin karfe 10 na dare, sun bude wuta babu kakkautawa a kan sansanin da ke yankin Shimfida a Karamar Hukumar Jibia ta jihar.

“Sansanin sojin yana Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Shimfida inda suka kashe soja daya da jami’in NSCDS daya nan take suka kuma jikkata wasu da dama.
“Sun kai harin ne a kan babura, kuma duk a kokarin jami’an tsaron, sai da maharan suka kashe mutum biyu suka jikkata wasu da dama sannan suka kona motoci biyu suka kuma tafi da wata mota wadda a ciki suka loka kayan abincin da suka sace wa mazauna kauyukan da ke yankin,” inji majiyar.

Ya kara da cewa jami’an tsaron da aka raunata a harin suna asibiti ana ba su kulawa.

Mai Magana da Yawun Hukumar NSCDC a Jihar Katsina, DSC Muhammad Abdara, ya tabbatar da rasuwar jami’in hukumar a harin, amma ba mu samu sojoji ba domin ji daga bangarensu.

Idan ba a manta ba, a watan Satumban 2021, ’yan bindiga sun yi wa ayarin wasu sojoji kwanton bauna a yankin inda suka kashe soja uku suka kuma jikkata wasu da dama.